Sada zumunci shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gareb su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk bangarde ne na sada zumunci. Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga dan uwa yayin haduwa da gaishe shi da ce masa yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi. Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da rike amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a boye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunci ne. Hukuncin sada zumunci: Wajibi ne Musulmi su sada zumuncin da ke tsakaninsu, kamar yadda shiryarwar ...