Hadin kai Mabudin ci gaban al-umma a kan Matsaloli daban-daban da kuma Cigaban su, kai baki dayama Duniya tana tafiyane a kan asasi na hadin kai. Kananan koramu da suke haduwa a wuri guda sune suke haifar da Babban kogi, ta yadda suke kasan-cewa masu karfi harsu rinka Samar da wutar lantarki, sannan su shayar da manya-manyan filaye na Noma,ta yadda wurare zasu koma kore shar, gwanin ban sha'awa.
Hakanan itaciya da ga sassa manya da kanana, kamar rassa da ganye, idan basu samu tushe daga saywa guda daya ba, to da ba za'a iya samun bishiyar ba. Hakanan makaranta da haduwar Malamai, da Dalibai, take cika.Hakanan Run-dunonin Sojoji masu Fada, Wadanda zasuyi nasara kayu nansu ba'arabe yakeba, sannan sun kaucewa duk wani sabani a tsakanin su, kuma suna biyayya ga shugaban su guda, Wanda yasan ya kamata, ta yadda zasu samu hadin kai mai karfin gaske a tsakanin su.
Amman waccar Rundunar da ko wanne daya daga cikinsu yake wani abu daban dana dan-uwan sa, tabbas ba tare da wani shakkuba za'aiya yin nasara akan su. To daman ko wacce al-umma idan ta samu kanta da ra'ayi daban-daban, ko kuma rashin biyayya ga shugabannin ta. Amman idan ana son samun nasara da ci gaban wadannan al-umma to lallai a samu wasu daga cikin al-umma, kuma su kasance masu kishin wadannan mutanen, wajen bada shawari na kwarai, domin kasan cewa tare.
Sannan duk wadan da suka hada Kansu ba'aiya shiga tsakanin su, kuma rashin tsaron da ake samu yana faruwa ta rashin hadin kai, saboda ta yayane mutum zai dauki makami ya kashe Dan-uwansa, inban da rashin hadin kai da sanin mutuncin Dan-uwansa sa. Idan kun zamo a guri guda to kowa zayyi sha'awar shiga cikin ku domin yasan akwai al-barka a tattare daku, kuma zaku iya cimma duk wata manufa da kuka saka agaban Ku, musamman ma ace kun kasance masu gaskiya, da bin doka.
Sabo da haka nake ganin samun hadin kai na al-umma, zai Samar da katon gari mai al-barka, da samun tsaro mai nagarta, da samun kwanciyar hankali ga talakawa, idan talakawan suka zauna lafiya, to shuwagaban ninta zasu zauna lafiya. Muna rokon Allah ya sanya al-khairi da samun hadin kai ga al-umma baki daya.
DAGA:
SANI ABUBAKAR DIKUWA
E-mail: saniabubakardikuwa7@gmail.com
08168604297
DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da y...
Comments
Post a Comment