Skip to main content

DEMOKRADIYA KENAN AYAU.

            Ko wacce Demokradiya ,ta ko wacce zamani, a ko wacce kasa  kuma a ko wacce al-umma, so take ta kusanto da Gwamnati kusa da jama'arta.Haka kuma babban burinta shine ayi dokoki da zasu dace da zamanin mutanen ta, a tsare dokoki bisa gaskiya, wannan ne dalilin fito da salon bawa jama'a damar su kafa jam-iyun siyasa,suyi musu sunaye da suka dace da kudurorin su.
              A kafa hukumar zabe mai cin gashin kanta, kowa ya zabi Dan takaran da yaga zai tsaremasa kudurorin sa, na gaskiya.a fafutikar zabe a fito da katin jefa kuri'a, wani lokaci kuma ayi yar tinke,domin tan-tance Wanda yayi nasara.kuma koda da kuri'a daya akafika to ka fadi. Saidai ba da sunan mutum mai gaskiya ake bawa hukumar zabe sunayen yan takara ba. Sunan gaskiya baro-baro baya daga cikin abubuwan da za'a tan-tance Dan takara akansu.
                A ganina da dai an zabi masu gaskiya, su nemo mafi gaskiya a cikin su.domin ya shugabanci al-umma, irin yadda Sarki yake yi a zaben shuwagaban sa na gar-gajiya,da babu batun ta zarce, ko ta lan-kwashe, da sauya sheka daga wannan jam-iyar zuwa wata jam-yar bata tasoba.A ganina Shugabanci na Dottawa ne, su sukafi kowa kusa da gaskiya. Idan an bawa dottawa zabo dottijo a cikin su  domin ayi aikin dottaku, da babu sauran aikin haya gaga.
                 Amman a yau an hada mashaya, da tsofaffin masu laifi,da fitattun marasa kunya, da sanannun maciya Amana, da gogaggun makaryata, da dakikan mutane, ace wai su zabo Shugaba.kaga anyi zagege kenan inji Dan Fulani daya fado daga bishiyar dabino ya zarce rijiya. Amman wa yafi gaskiya sanin gaskiya, ai matar aure tasan mijin ta ko a cikin daji ta ganshi ,komai taron maza tana iya bam-banceshi. Tabbas da kin gaskiya sai bats.
                   To Amman anya Demokradiyar mu batashiga  wannan halin kuwa. Allah ya kyauta.
          
         Sani Abubakar Dikuwa
              08168604297

Comments

Popular posts from this blog

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da y...

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All...

ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM KASHI NA BIYU

 Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2) DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin. A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin ƙoƙon kai, da kuma wadda ke ƙasan ƙeya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take ƙasanta, wadda ta haɗe da laaka dake gadon bayan mutum. Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin ƙoƙon kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta ɓari biyu ce: ɓarin hagu da ɓarin dama. Wasu masanan sun ce aikin da ƙwaƙwalwar dama ta ke yi...