Allah ya kawo mu damuna kuma muna fatan Allah ya sanya al-barka a wannan damunar tamu ta bana. Abun dake faruwa shine mafiya yawa daga manoman mu, suna batun akan chewa wai amfanin noman da sukayi bara baiyi kudiba, ko kuma baiyi tsada ba, shine dalilin dayasa wasu ke cewa bazasu suka abunda suka shukaba bara.
To Amman kuma idan kukayi duba akan abunda suka shuka baran ai baiwuce Masara, Gero, dawa, da shinkafa ba. To Amman kuma suna cewa wai bazasu sake sukawaba a wannar shekarar, sai naga kuma ai wannan abincin sune da idan babushi ake shiga matsar Rayuwa. Kusanifa duk wata damuwa matukar a kwai lafiya,to babu wani abu da mutum ke bukata kamar abinci.
Sanna mafa duk Gwa-gwar mayar mutanen mu na arewa bai wuce akan abunda za'aciba, domin kuwa idan kana da abinci a gidan ka, to sauran al-amuran Rayuwa za'a iya hakuri da wasu. Don haka ba dadai bane ace za'a kaurace wa ban-garen abinci a nausa ban-garen Neman kudi muraran ba.kuma idan har muka koma noman abunda zai kawo kudin ai sai idan Gwamnati tanada yadda zata sarrafa wannan abun da muka noma tukunna zaiyi tsadar ta ake burin akai.
Munan yan Arewa babu wani abu daya dace damu, kuma akasan mu dashi face NOMA DA KIWO. Aima wannan shine martabar mu aduniya baki daya. Idan muna bukatar mu Noma kayan kudi to wannan lallai sai idan Gwamnati ta saka mana hanu acin lamarin, ta hanyar kawo injunan da zasu sarrafa abun da muka Noma,sannan Gwamnati ta bamu kayan noman na zamani, wadanda suka hada da IRIN NOMA,TAKI AKAN LOKACI,DA KUMA TALLAFI. Idan mun samu wadannan to kunga zamu noma abincin mu, zamu noma abunda akeso na kudi.Amman yanzu Gaskiya garajene.
Sabo da yin hakan zaisa mu fuskanci tsadar Rayu, da kuma yinwa a kasa baki daya.kuma talaka shi zaifi kowa shan wahala saboda komai ya faru naga talaka yafi shan wahala. Shawara ta dai anan shine kada mubar abunda muka sani, mutafi neman abunda baya da tabbas.
SANI ABUBAKAR DIKUWA.
08168604297
WATAN SHA'ABAN: SALLOLIN DARAREN SHA'ABAN: DAREN FARKO: An karbo daga Manzon (S) ya ce: "Wanda ya yi sallah a daren farko na Sha'aban raka'a (12) a kowace raka'a ya karanta Fatiha (1) Kulhuwa (15) Allah zai rubuta masa ladar ibadar shekara goma sha biyu. kuma za a gafarta masa zunubbansa kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi" (Dhiya'us Saliheen.29). SALLAH TA BIYU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa(30) Idan an sallame a ce: Allahummah Haaza Ahdiy Indaka Ila Yaumil Kiyamah".Wanda ya yi wannan sallah. Allah zai kare shi daga tarkon shedan da rundunarsa. kuma ya ba shi ladar Salihan bayi. (Dhiya'u.29). SALLAH TA UKU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (11) Wanda ya wannan sallah. Allah zai tsre shi daga sharrin halittun sammai da na kassai. kuma zai gafarta masa zunubbai Subu Saba'in na kaba'irah da ke tsakaninsa da shi Allah. DARE NA BIYU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha ...
Allah ya saka
ReplyDelete