Skip to main content

Posts

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da yayi.
Recent posts

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All

ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM KASHI NA BIYU

 Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2) DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin. A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin ƙoƙon kai, da kuma wadda ke ƙasan ƙeya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take ƙasanta, wadda ta haɗe da laaka dake gadon bayan mutum. Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin ƙoƙon kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta ɓari biyu ce: ɓarin hagu da ɓarin dama. Wasu masanan sun ce aikin da ƙwaƙwalwar dama ta ke yi, ya

ƘWAƘWALWAR DAN ADAM KASHIN FARKO

Ƙwaƙwalwar ɗan’adam Editor  March 26, 2023 DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai mabambanta, domin ku fa’idantu. Rubtun yau zai mayar da hankali ne akan ƙwaƙwalwar ɗan adam, baiwar da Allah yayi mata, da wasu daga cikin baye- bayenta. Ƙwƙwalwar ɗan adam tana waɗansu baye-baye da Allah yayi mata a jiki saboda muhimmancinta. Bari na kawo kaɗan daga ciki. Matsayi: Ƙwaƙwalwar ɗan adam ta kasance a mafi ɗaukakar bigire a jikin ɗan adam. Da Sarkin halitta Ya tashi, sai bai sanya ƙwaƙwalwa a kogon ƙirji ba, ko kogon ƙugu; a a, sai Ya sanya ta a cikin ƙoƙon kai, kuma a bigiren da ta zamo sama da kowace gaɓa a jiki. Sama take da ido, sama take da hanci, baki, da dukkan fuska. Ƙwaƙwalwa sama  take da duk wata gaɓa a jiki. Wannan tsari ya bada ma’ana sosai, saboda bigiren da ƙwaƙwalwa take, da aikin da ta ke yi ya dace da kasancewar ta shugaba ko jagorar gudanarwa

SALLOLIN NAFILA NA WATAN SHABAN.

 WATAN SHA'ABAN: SALLOLIN DARAREN SHA'ABAN: DAREN FARKO: An karbo daga Manzon (S) ya ce: "Wanda ya yi sallah a daren farko na Sha'aban raka'a (12) a kowace raka'a ya karanta Fatiha (1) Kulhuwa (15) Allah zai rubuta masa ladar ibadar shekara goma sha biyu. kuma za a gafarta masa zunubbansa kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi" (Dhiya'us Saliheen.29).  SALLAH TA BIYU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa(30) Idan an sallame a ce: Allahummah Haaza Ahdiy Indaka Ila Yaumil Kiyamah".Wanda ya yi wannan sallah. Allah zai kare shi daga tarkon shedan da rundunarsa. kuma ya ba shi ladar Salihan bayi. (Dhiya'u.29). SALLAH TA UKU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (11) Wanda ya wannan sallah. Allah zai tsre shi daga sharrin halittun sammai da na kassai. kuma zai gafarta masa zunubbai Subu Saba'in na kaba'irah da ke tsakaninsa da shi Allah. DARE NA BIYU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha

START YOUR FISH FARMING❓

SANI ABUBAKAR DIKUWA IN A FARM. Contents Chapter 1 Introduction   Chapter 10 Taking Care of your Pond Chapter 2 Locating your Fish Farm   Chapter 11 Taking Care of your Fish Chapter 3 Constructing Fish Ponds   Chapter 12 Harvesting your Pond Chapter 4 Inlets to Let Water into the Pond   Chapter 13 Beginning Again Chapter 5 Outlets to Let Water Out of the Pond   Chapter 14 Improving Farm Management Chapter 6 Bringing Water to your Ponds   Chapter 15 Producing Fish in Pens Chapter 7 Controlling the Water in the Pond   Chapter 16 Producing Fish in Cages Chapter 8 Preparing your Pond   Chapter 17 Your Farm and your Fish Ponds Chapter 9 Stocking your Pond with Baby Fish   Chapter 18 Keeping you and your Family Healthy     Test your Knowledge     1. INTRODUCTION   What is fish farming? Why do we raise fish? What do you need to raise fish? How do we begin? 2. LOCATING YOUR FISH FARM   Where to put your fish pond Water supply Soil quality Testing soil 3. CONSTRUCTING FISH PONDS   How large sho

NOMAN KIFI

  Yadda ake fara noman kifi A gaskiya ma, bayanin kyau ya bambanta daga mutum zuwa mutum. Duk da haka, idan aka ambaci kwayoyin ruwa musamman kifaye a cikin tafki mai kyau, kowa yana ganin su suna da ban sha'awa. Duk da yake yana iya yin sauti duka hadaddun zuwa raya kifin, a nan, za mu ɗauke ku wannan tsari mataki-mataki don tabbatar da cewa ba kawai kayan aiki ne kawai ba amma har ma da kuzarin fara noman kifi. Cike da sha'awa, goyan bayan gwaninta, muna juyar da duk ra'ayoyinku da zaburarwa zuwa ga nasara mai ban sha'awa. Menene noman kifi? Mahimmanci, noman kifin da aka fi sani da pisciculture tsarin ciyar da halittun da ke zaune a cikin ruwa na kasuwanci ko dai a cikin yanayi mai sarrafawa ko kuma ba a sarrafa shi ba don ƙara yawan aiki. Yadda ake fara noman kifi mataki-mataki Kifin kifin tsari ne sosai. Kamar yadda aka ambata a baya, muna ɗaukar ku da gwaninta tun daga lokacin da kuka zaɓi wurin da kuke son adana kifi har zuwa mataki na ƙarshe inda zaku tallata sh