A Hausan ce Gaskiya itace Amana. Wanda duk yarasa Gaskiya to ya rasa Amana. Wanda baya da Amana,ba tare da Gaskiya yake tafiya ba. Awajen mutanen kwarai mai Gaskiya ake bawa Amanar tsaron dukiya, shi ake shugabantar wa ga shaidar bashi, da rance, da aro, da jin-gina, da kyauta, da musaya, da duk wani aikin da ake jiran lokacin sa. Mai Gaskiya akebawa sako, da ajiyar tsintuwa a samesu yadda suke.
Ire-iren wadannan darojoji na mai Gaskiya sune fal-safar karuruwan magana da dama da akeyiwa mai Gaskiya. Sannan mai Gaskiya bazai zama mai Gaskiya ba sai ya nisanci son Rai,da hakurin rikon Amana a lokacin da rikonta yake da tsananin wahala ga mai riketa,da sauran jama'a. Idan jama'a sukaga wuyar abun, sannan Wanda suka tunkara ya rike musu, to lallai zasu aminta da yafisu,ya can-canci kuma ya jagorance su.
Gaskiya mafitace a duk inda kashiga,kuma tutace da take tallar mai ita a duk inda yake,sannan kuma abace mai daci ga Wanda baida ita. Allah ka al-barkaci Rayuwar mu, kuma kasanya mu zamo masu Gaskiya da Amana.
Marubuci Sani Abubakar Dikuwa.
08168604297.
WATAN SHA'ABAN: SALLOLIN DARAREN SHA'ABAN: DAREN FARKO: An karbo daga Manzon (S) ya ce: "Wanda ya yi sallah a daren farko na Sha'aban raka'a (12) a kowace raka'a ya karanta Fatiha (1) Kulhuwa (15) Allah zai rubuta masa ladar ibadar shekara goma sha biyu. kuma za a gafarta masa zunubbansa kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi" (Dhiya'us Saliheen.29). SALLAH TA BIYU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa(30) Idan an sallame a ce: Allahummah Haaza Ahdiy Indaka Ila Yaumil Kiyamah".Wanda ya yi wannan sallah. Allah zai kare shi daga tarkon shedan da rundunarsa. kuma ya ba shi ladar Salihan bayi. (Dhiya'u.29). SALLAH TA UKU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (11) Wanda ya wannan sallah. Allah zai tsre shi daga sharrin halittun sammai da na kassai. kuma zai gafarta masa zunubbai Subu Saba'in na kaba'irah da ke tsakaninsa da shi Allah. DARE NA BIYU: Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha ...
Comments
Post a Comment