Hakuri;wani al-amarine mai matukar tsada musamman ga Wanda bashi da Juriya. Hakuri a rayuwa yana da matukar girma idan har ya kasan ce da yafiya. Mafi yawan tashin hankalin da yake kawo fada tsakanin ma'aurata, rashin hakuri ne. Hakama idan kaga an samu tashin-tashina a gari, to shima ya samo asaline daga rashin hakuri. Haka idan an kaure da yaki tsakanin kasa,da kasa wannan ma rashin Hakuri. Inda ace kowa zai hakura, kuma ya tsaya a matsayin sa da an huta da samun tsaiko a tsakanin al-umma. Talaka ya hakura da talaucin sa, ya gane cewa wannan shine ya dace da jarrabawar sa, daga Allah. Mai Dukiya ya hakura da dukiyar daya samu, ya taimaka wa Wanda bashi dashi,ko kuma na kasa dashi. Mai mulki ya hakura da matsayin sa, Wanda Allah ya bashi, yayi adalci acikin al-umma, kuma ya gode da kimar daya samu a cikin mutane. Malami yayi hakuri ya jure wajen karantar da jama'arsa wajen sanin dokoki, kuma ya jure da matsayin sa na mai hurda da masu koyo. Idan da za'ayi haka da kowa zai fahimci ta inda zai taimaki dan-uwansa, kuma da babu batun rashin godiya, ko kuma Tara dukiyar da bazata amfani mai itaba balle Wanda yake hangen an cuceshine wajen tara wannan dukiyar. Da kowa zai iya yiwa dan-uwansa nasiha kuma ya yarda. Sannan da ansamu cigaba mai dimbin yawa, da karuwar zaman lafiya.
Allah ka sanya mu, muzama bayin ka masu hakuri, da Juriya.
Amee
Sani Abubakar Dikuwa
08168604297
Allah ka sanya mu, muzama bayin ka masu hakuri, da Juriya.
Amee
Sani Abubakar Dikuwa
08168604297
Comments
Post a Comment