Sheikh Ibrahim zakzaky ne ya kafa kungiyar shi"a ta kasa, wato IMN a arewacin kasar a birnin Zaria dake a jihar Kaduna a shekar 1980 da 1990. Ya samu wannan hurumi ne ta kwaikwayo da yabo ga juyin juyahalin kasar Iran a 1979 tare da mu'amala da hotunan Ayatullah Ruhollah Khomeini da Ayatullah Ali khamenei a shafinsa na yanar gizo. IMN na kuma goyon bayan kafa gwamnatin Islama a Nigeria. IMN ta dade da kasancewa a bar lura wajen rikici ga gwamnatin Nigeria, wadda ta aiyana IMN a zaman kungiyar rikici tare da anfani domin danne mabiya IMN da duk wani auyukan ta.
Sama da shekara goma tun sanda a ka dakile kungiyar IMN--kisan gilla, tare da binne mabiya IMN 347 da hukumar sojojin Nigeria sukayi. A Disamba 2015 a Zaria-kuma duk da cewa COL a jihar Kaduna a 2016 sun dora alhakin a kan sojoji da kuma shawartar cewa a gurfanar da wadanda suka aikata laifin, Amman babu wani jami'in soja da aka kama domin yin bayani.
A 2018 yan sandan Nigeria sun cigaba da tsare fitaccen malamin su, sheikh zakzaky, da matar sa malam zeenah Ibrahim, wadan da ake rike dasu batare da gurfanar da su ba, tun Disamba 2015, duk da cewa babbar kotun tarayyar Nigeria a abuja tayi Ummarni a ranar 2-12-2016, cewa a sake su tsakanin kwana 45. Hukomomi kuma sun kama a kalla mabiya IMN 15 a 2018.
Gabadaya 2018, mabiya IMN sunyi zanzanga a fadin kasar suna bukatar a saki sheikh zakzaky. A Kaduna da sokoto hukomomin jihohin sun haramta IMN tare da Ibadun su. Kafar labarum IMN na nuni da cewa wasu lokuta ana anfani da tsananin karfi domin domin tarwatsa zanzanga, Wanda ke jawo raunuka da mutuwa a wani lokaci.
Tsakanin Oktoba 28, da Nuwamba 1,Musulmai yan Shi'a sunyi tattakin a fadin kasar domin gudanar da Arbaeen-wani bikin addini na Shekara-shekara da yan musulmai, yan Shi'a ke gudanarwa a fadin duniya baki daya domin tunawa da mutuwar Imam Hussein a karni na bakwai. Daruruwan yan Shi'a sunyi tattaki a abuja domin girmama bikin da kuma zanzangar sakin sheikh zakzaky. Kodayake sojojin Nigeria sunce masu zanzangar sun jefi jami'an tsaron Nigeria da duwatsu a abujan.
Babu wata shedar dake nuna tashin hankali a tare da mabiya IMN. Sojojin Nigeria sunyi harbe-harbe a cikin jama'a inda suka kashe a kalla mutane 45,kamar yadda kungiyoyin kare hakkin Dan-Adam suka fada. Babu wani jawabi daga gwamnatin Nigeria dake aibata abun da sojojin ta suka aikata akan Wannan anfani da tsananin karfi a kan masu zanzangar lumana. Da farko hukomomi sojojin Nigeria ta aika da sakon Twitter tana mai kare abinda sojojin ta suka aikata,daga baya kuma ta share sakon Twitter data rubuta.
To abunda mukeso mu hanga anan shine, ya kamata hukomomin Nigeria idan zasu dauki mataki akan al-ummar kasa, to ta dauki matakin da kowa zai tayata wajen kokarinta, da kuma daukar darassi ga wasu masu son sunyi irin wannan laifin idan har laifine daya shafi kasa bakidaya,ko kuma kwantar da yarzomar da ta taso a cikin kasa. Sannan kuma su dauki duk yan-kasa amatsayin yan-Nigeria wajen yanke hukunci.
Sannan su kuma yan-uwa yan kasa bakidaya ya kamata mugane cewa kowacce kasa tana da nata dokokin daya zama dole abisu musamman ma al-amarin tsaro, kuma idan har zamu zama masu tayar da hankalin kasar mu tofa babu batun cigaba, sabo da kullum shuwagabannin mu, suna fama da matsalar tayaya zasu kwantar da tarzomar da muka tayar a cikin kasa.
Yanzu idan kun duba abun da yafaru da su yan-uwa yan Shi'a, ai abun bai kamata ba ace ana kashe yara, mata, da wasu matasan mu na kasa. Wanda muke fatan suzamo manyan gobe, sai gashi a yau suna rasa rayukan su. Sannan itama gwamnatin Nigeria da yakata ta duba abun dake faruwa a wata fuskar, tagane cewa wadannan mutanen suna fafutikar sune akan abunda sukayi imani dashi a addinan ce. Idan kuma akace wannan addinine to yana da wahala ka iya juya tunanin su akai.
Saboda haka jama'a da dama sun bayar da shawarar a saki malamin nasu, sannan akafa masa wasu dokokin da ake ganin ya takasu a baya.kuma ya kamata a gujewa duk wani tashin hankalin da yake haifar da asarar dukiya, da rayukan yan kasa. Sannan kuma a kiyaye duk wata doka da ta bayar da damar kowa yayi addinin sa yadda ya kamata, sannan sai ayi dokar yada addinin ta yadda baza'a samu wasu masu dora matasan mu akan wani al-amari mai kama da son zuciya ba.
Alhamdulillahi. Nan zamu tsaya sai wani mako zamu cigaba daga inda muka tsaya.
Sani Abubakar Dikuwa
08168604297
Comments
Post a Comment