Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2)
DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA
‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin.
A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta.
Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin ƙoƙon kai, da kuma wadda ke ƙasan ƙeya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take ƙasanta, wadda ta haɗe da laaka dake gadon bayan mutum.
Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin ƙoƙon kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta ɓari biyu ce: ɓarin hagu da ɓarin dama. Wasu masanan sun ce aikin da ƙwaƙwalwar dama ta ke yi, ya banbanta da aikin ƙwaƙwalwar hagu.
Ƙwaƙwalwar hagu ita ce mai nazari akan abubuwan rayuwa, lissafi, shirakawa ko tsara al’amura, yarda da zahiri, naɗe ilimin Kimiyya, da naƙaltar gaskiyar zance. A ɗaya ɓangaren kuwa, ƙwaƙwalwar dama ita ce mai tasirantuwa da zane, ƙirƙirar abubuwa, hasashe, mafarkan rayuwa(misali ace ayi ruwan tsabar kudi daga sama), labaran ƙirƙira, zantukan rai( misali mutum ya dinga raya wani abu a ransa), fahimtar saƙonni( Wanda ba a fada da baki, saƙonni da ake aikawa da ido, gira, hannaye, da sauransu).
Haka kuma ƙwaƙwalwar dama ce ke kula da ɓangaren hagu na jikin ɗan adam; ita kuma ƙwaƙwalwar hagu ta sarrafa ɓangaren dama na jikin ɗan Adam. Idan kuka lura da kyau, mutane sunfi amfani da hannunsu na dama fiye da na hagu. Kenan in haka ne sunfi amfani da ƙwaƙwalwar hagu fiye da ta dama. Shi yasa sai ka ci karo da badame tara kafin ka ci karo da bahago ɗaya. Wannan na nuna cewa kaso casa’in cikin ɗari na mutane na amfani ne da ƙwaƙwalwar hagu tunda ita ce ke sarrafa hannun dama, sannan kuma kaso goma na amfani da ƙwaƙwalwar dama.
Ita wannan ƙwaƙwalwa mafi girma wato “cerebrum” nauyinta ya kai kilogram 1 da ɗigo biyu; spa sauƙaƙe, nauyinta sai kai nauyin ƙatuwar abarba guda ɗaya koma ya fi. Ita ce ta lashe kaso 87 cikin ɗari na nauyin dukkan ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Wato sauran guda biyun (ta ƙasan zeya da kuma wadda ta haɗe da laaka, sun ɗauke kaso 13 ba nauyin ƙwaƙwalwa).
Wannan ƙwaƙwalwa tana ɗauke da mafi yawan ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa fiye da na sauran. Daga cikin muhimman siffofinta akwai: Tunani, Nazari, Hikima, La’akari, Hankali, sanin-ya-kamata, Ilimi, ƙirƙira, Fasaha, Naƙaltar harshe, Azanci, Hukunci, da makamantansu. Wannan ita ce ƙwaƙwalwar da ta sanya ɗan Adam ya yi wa sauran halittu zarra!
Bari mu tafi izuwa ƙwaƙwalwa ta biyu: wadda ke ƙasan ƙeya, daidai inda wuya ya haɗu da Kan mutum. Ita wannan ƙwaƙwalwa, da turanci ana kiranta da “cerebellum”. Ita ma tana da ɓangaren dama da ɓangaren hagu. Daga cikin muhimman ayyukanta akwai sarrafa motsi kamar su tafiya, gudu, tsalle da irinsu. Ita ce ke kula da daidaito a jikin ɗan Adam. Idan mutum ya tsaya kyau, to da hannunta a ciki. Saboda tana hana ɓarin jikin dama ya rinjayi na hagu, ko kuma ɓarin jikin hagu ya rinjayi na dama.
Sannan tana taimakawa wajen sanar da mutum halin da yake ciki. Ta yadda mutum zai gane cewa: yanzu fa a tsaye nake; ko a zaune nake; ko a kwance, ko kuma a tafiye nake, ko magana nake. Meye amfani hakan? Saboda kowanne motsi da ]an Adam zai yi, na da muhallinsa. Misali: kula da motsin harshenki ko harshenka, tsokar fuskarka, da ta idanunka lokacinda kake ƙoƙarin magana domin idar da wani saƙo. Tuƙin mota, babur ko keke na da irin nasu motsin. Ga kuma motsi na musamman mai buƙatar tattara hankali waje guda: irin su rubutu, tiyata, saƙa, sa sauransu.
Wannan ƙwaƙwalwa ita ce ke taimaka wa ɗan Adam wajen sanin ina ne samansa, ina ne ƙasansa, ina ne hagunsa da kuma ina ne damansa, musamman wajen sauti ko motsin wani abu. Ɗan Adam zai iya fahimtar cewa sautin da yaji na hon ɗin mota daga hagunsa yake ko daga damansa; haka kuma zai iya fahimtar cewa sautin jirgin nan da yake ji a saman kansa ne daga hagu ko dama. Ma’ana shi ɗan Adam zai iya tantance daga wane sashe wannan sauti ke fitowa.
Haka dai wannan ƙwaƙwalwa na taka muhimmiyar rawa wajen sanya ɗan Adam yaji wani abu a ransa sakamakon wani abu da ya faru da shi: jin tsoro, jin farin ciki, jin baƙin ciki, jin dadi, jin soyayya, jin mazabura, jin ƙunci da ire-irensu.
Idan wannan sashe na ƙwaƙwalwa ya samu matsala a sanadiyyar haɗari, ko cutar daji, ko shan giya, ko shan miyagun ƙwayoyi, ko shan wani abu da zai iya kasance wa guba a tare da ita, to tabbas ɗan Adam zai shiga matsala. Alamun su haɗar da: rashin iya tafiya a tsanake, shan wahala wajen gudanar da motsi na musamman kamar su raɗa, sigina, rubutu, tuƙin abin hawa da sauransu. Karkarwar hannaye da harshe lokacin yin magana, ko mutum yaji kamar garin yana jujjuya masa, wato ya dinga jin hajijiya.
Ɓangare na uku na ƙwaƙwalwa shi ake Kira da “brainstem” a turance. Ta na a saman wuya ta baya, kuma daga ƙasanta haɗe take da laaka wadda take a tsakiya gadon baya, cikin ƙashin baya. Wannan ƙwaƙwalwa na da cibiyoyi masu tabbatar da kasancewar ɗan Adam a raye.
A cikinta akwai:
1.Cibiyar numfashi. Ita ce ke kula da numfashin ɗan Adam, wanda a cikin kwanciyar hankali, ɗan Adam yana numfashi sau Goma zuwa sau Goma sha biyar a duk minti ɗaya. A lokacin da ɗan Adam ya ji tsoro, ko yake motsa jiki, ya na yin numfashi fiye da haka a duk minti ɗaya.
Akwai kuma cibiyar Zuciya. Wannan cibiya na da tasiri a kan zuciya. Idan bugun zuciya yayi ƙasa, za ta iya ƙara shi, ko kuma idan yayi yawa, za ta iya rage shi. Amma ba ita ce ke sanya zuciya ta harba ba. Aikin wannan cibiya shi ne daidaita harbawar da zuciya ke iya duk minti ɗaya. Zuciyar ɗan Adam na harba jini duk sassan jiki sau 70 zuwa sau 100 a duk minti ɗaya. ko sama da haka lokacin da mutum yaji tsoro, ko yoshida wani yanayin firgici, ko motsa jiki. Amma akwai bambanci tsakanin mutane. Wani Zuciyarsa sau 85 take harbawa, wani sau 71, wata sau 96. Duk wannan babu komai matuƙar bai wuce sau 100 ba a halin da mutum ke cikin kwanciyar hankali.
Masu karatu mu haɗu a mako mai zuwa idan Allah ya kai mu, domin ci gaba da kawo mu ku bayani game da jikin ɗan adam. Kafin nan na ke cewa, assalamu alaikum.
Daga naku SANI ABUBAKAR DIKUWA
Comments
Post a Comment