Skip to main content

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa.

Bismillahirrahmanirrahim,

Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu.

Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki:

* Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277]

* Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280]

* Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7]

* Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904]

* Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da yayi. [Silsilatul Saheha 1797]

* Azumi zai yi ceto a ranar hisabi inda zai ce: “Ya Ubangiji, na hana shi abincin sa, da abubuwan da yake bukata bayyanannu a lokacin yini, a bar ni in cece shi” [Sahehul Targib, 1/407]

* Warin bakin mai Azumi yafi kamshi a wurin Allah SWT akan turaren Miski [Sahihu Muslim, 2/807]

* Azumi kariya ne da yake nesantar da mutum daga azabar wutan jahannama. [Saheehul Jaami 3880]

* Duk wanda yayi azumi na kwana daya saboda Allah, Allah SWT zai nesantar da fuskar sa tazarar shekaru 70 daga wuta. [Sahihu Muslim 2/808]

* Duk wanda yayi azumi na kwana daya don neman falalan Ubangiji, kafin ya buda baki ya koma zuwa ga Allah, to zai shiga Aljannah [Saheehul Targib 1/412]

* A cikin Aljannah akwai wani kofa mai suna Al’Rayyan, babu wadanda zasu shige ta sai masu azumi. [Sahihul Bukhari 1797]

* A cikin watan Ramadaan ne Allah SWT ya saukar da AlQur’ani, kuma a cikin ta ne daren Lailatul’Qadr yake, wanda Allah SWT yace daren yafi watanni dubu.

* Duk lokacin shan ruwa bayan azumi, Allah yana zaban bayin sa wadanda zai ‘yanta daga wuta. [Saheehul Targhib 1/419].


Sai mun sake haduwa a wani rubutun.

Comments

Popular posts from this blog

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All...

ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM KASHI NA BIYU

 Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2) DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin. A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin ƙoƙon kai, da kuma wadda ke ƙasan ƙeya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take ƙasanta, wadda ta haɗe da laaka dake gadon bayan mutum. Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin ƙoƙon kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta ɓari biyu ce: ɓarin hagu da ɓarin dama. Wasu masanan sun ce aikin da ƙwaƙwalwar dama ta ke yi...