FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN
Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa
DAGA: Sani Abubakar Dikuwa
Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah.
Daga cikin falalar azumin sun hada da:-
1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).”
2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578).
3. Azumi kuma shine Musababin tsoron Allah.
4. A watan Ramadan ana bude kofofin gidan Aljanna, sannan kuma ana kulle kofofin gidan wuta sannan a daure shaidanu kamar yadda ya tabbata a hadisin Abi Huraira. (Kuduba Sahihul Bukhari 1899).
5. Hadisi ya tabbata wanda Imam Tirmizi ya ruwaito cewar Manzon Allah {S.A.W.} yace: "Warin bakin mai azumi yafi kamshi fiye da turaren Al-miski a wurin Allah." Hadisi ne sahihi.
6. Yazo a hadisai da dama cewa: Dukkan aikin Dan Adam nasane Malaikune suke rubuta shi, amma azumi wannan na Allah ne Shi Yake sakawa wanda yayi shi (hadisin ya tabbata acikin targhib wattarhib, juz'I na farko shafi na 75).
Muhadu a wani karon nagode Allah ya karbi ibadah.
Comments
Post a Comment