Skip to main content

ƘWAƘWALWAR DAN ADAM KASHIN FARKO


Ƙwaƙwalwar ɗan’adam

DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA

’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai mabambanta, domin ku fa’idantu.

Rubtun yau zai mayar da hankali ne akan ƙwaƙwalwar ɗan adam, baiwar da Allah yayi mata, da wasu daga cikin baye- bayenta. Ƙwƙwalwar ɗan adam tana waɗansu baye-baye da Allah yayi mata a jiki saboda muhimmancinta. Bari na kawo kaɗan daga ciki.

  1. Matsayi: Ƙwaƙwalwar ɗan adam ta kasance a mafi ɗaukakar bigire a jikin ɗan adam. Da Sarkin halitta Ya tashi, sai bai sanya ƙwaƙwalwa a kogon ƙirji ba, ko kogon ƙugu; a a, sai Ya sanya ta a cikin ƙoƙon kai, kuma a bigiren da ta zamo sama da kowace gaɓa a jiki. Sama take da ido, sama take da hanci, baki, da dukkan fuska. Ƙwaƙwalwa sama  take da duk wata gaɓa a jiki. Wannan tsari ya bada ma’ana sosai, saboda bigiren da ƙwaƙwalwa take, da aikin da ta ke yi ya dace da kasancewar ta shugaba ko jagorar gudanarwar gaɓɓan ɗan adam.
  2. Kariya: Sarkin halitta ya bawa ƙwaƙwalwa kariya ta musamman, kamar yadda ya bawa sauran manyan gaɓɓai masu matuƙar muhimmanci irin rasu kariyar. Misali: (a) Zuciya tana cikin kariyar ƙasusuwan haƙarƙari. (b) Jariri ko jaririya lokacin da suke cikin uwa, akwai kariya ta musamman da Allah yayi musu. Shi yasa a cikin littafi mai girma Ubangijin halitta yake cewa: “Mun halicci ɗan’adam cikin duffai 3”. A kimiyyace, jinjiri a kewaye yake da abubuwa guda 3: Na ɗaya, bangon cikin uwa; na biyu, bangon mahaifa; na uku itace jakar paya wadda ta kewaye jaririn. Kuma kowacce gaɓa da muka lissafa anan, hijabi ce kuma kariya ga jinjirin da ke ciki. 
    To haka ita ma ƙwaƙwalwa Allah ya bata kariya sosai. Kamar yadda na ce, a cikin ƙoƙon kai take, Wanda a turance ake kira da “skull”. Yadda wannan ƙashi yake da ƙwari ma wasu masanan na cewa ya kai ƙwarin kankare na gini!

Bayan kariyar ƙashi, ƙwaƙwalwa na kariyar tantani har ruɓi uku(3). Sannan bayan wannan, hanyoyin jinin da suka baibaye ta na da shamaki tsakaninsu da ƙwaƙwalwa, don gudun kada wani abu ya biyo jini, daga nan kuma ya faɗa ƙwaƙwalwa. Saboda tasirin wannan kariya, har ma wasu magugunan cutukan ƙwaƙwalwa kan gaza isa cikin ta, matuƙar dai mutum ta baki ya sha ƙwayar maganin ko kuma allurar maganin akayi masa/mata.
 

  1. Tasaruffi: Ubangijin halittu ya bawa ƙwaƙwalwa dama da iya sarrafa sauran gaɓɓan ɗan’adam. Duk da cewa wannan bayani ya kamata in kawo shi a sashen ayyuka da ƙwaƙwalwa ke yi, to amma ya fi dacewa in sanya shi a nan. A kafatanin jiki, babu wata gaɓa da ke sarrafa dukkan gaɓɓai idan ba ita ba. Hamma, atishawa, miƙa,  yunwa, duk da  hannunta a ciki. Babu yadda za ayi ace wai ƙodarka ta kula da yanayin numfashinka, ko ta shirya tsare tsare na narka abincin da ka ci! Wannan aiki sai ƙwaƙwalwa.
  2. Tsari: wato
    ƙwaƙwalwar ɗan Adam tana da tsari mai matuƙar ban sha’awa. Tana tsara abu daki daki, daga wannan sai wannan. Shi ya sa mutum ya fi sauran halittu hankali saboda ƙwaƙwalwarsa na iya tsara masa abubuwa daki-daki. Misali, abu mafi muhimmanci da ta fi bashi kulawa shi ne sukuni! Duk abinda za ka aiwatar, matuƙar ba sukuni a ciki, to a mafi yawan lokaci, kwaƙwalwar ka zata ta iya haƙura da wannan abu ko meye shi. Misali, kana jin bacci sosai, ga kuma kana so kayi karatun makaranta,  ba ka yi aune ba, za ka iya jin bacci ya kwashe ka. Ko kuma kina tare da ƙawarki kuna hira mai dadi, amma kuma rabon ki da abinci tun jiya da yamma. Akwai gaɓar da za a je dole ke katse hirar, ki nemi abinci domin ki kori tabahuwa!
  3. Ɗabi’a: Allah ya halicci ƙwaƙwalwar ɗan’adam domin ta gane abubuwa saboda ta sauƙaka wa ɗan’adam gudanar da sauran harkoki na rayuwarsa. Da zarar kayi wani abu sau ɗaya, biyu, uku, huɗu, to fa ƙwaƙwalwar ka za ta ɗauki haske cewa wannan abu ana buƙatar sa a rayuwa, saboda haka sai ta fara mayar da shi ɗabi ‘a; sawa’un abun nan nai kyau ne ko akasi haka. Duk inda ɗan Adam ya samu wata biyu zuwa uku, ya na yin wani abu kullum, ta abun zai zama dabi’a. Mutum zai dinga gudanar da wannan abu ba tare da ya yi dogon tunani ba.  Misali idan ɗan adam ya koyi tafiya, sa zarar ya iya to ya dena tunani akan ya ake ayi tafiya. Ƙwaƙwalwar sa tuni ta ɗau hakske, ta adana dukkan bayanan yadda ake tafiya. To da zarar ya tashi zai yi tafiya, sai kawai ƙwaƙwalwar ta bijiro da wannan bayani ta kuma yi tasarrufinsa, ba tare da wani tunani ba.
     
  4. Azanci: Ɗan Adam yana da fifiko akan sauran dabbobi saboda azancinsa. Wato kamar “creativity” kenan a turance. Azancin ɗan Adam na cikin ƙwaƙwalwarsa. Kuma wannan baiwa ta azanci ta taimakawa ɗan Adam wajen zama abinda ya zama a yau. A tarihin ɗan Adam, ya kasance yana bijiro da dabaru kala-kala waɗanda za su taimake shi wajen saukaƙa rayuwarsa, da kuma tabbatar da sukuni. Ɗan Adam ya ƙirƙiri abubuwa da dama ta hanyar amfani da azancin ƙwaƙwalwar sa kamar su: Gina gida, ƙera mota, ɗinka kaya, haɗa kujera, gado, kwalla,  matashi. A wannan zamani,  azancin ƙwaƙwalwar ɗan Adam wanda Allah ya bashi, ya sa ya iya ƙirƙirar jirgin sama,  kwamfuta, wayar salula, Injin wankin kaya, injin cire kudi, na’urar tiyata, da makamantansu.
     
  5. Hikima: sabin kowa ne cewa, duk wani mai hikima, to tabbas yana da kaifin ƙwaƙwalwa. Kuma Ubangiji na cewa:” duk Wanda a ka bashi hikima to haƙiƙa an bashi alkhairi mai girma.” Wannan na ɗaya daga cikin baiwar sa Allah yayi wa ƙwaƙwalwa akan sauran gaɓɓai. To ta ina ake samun hikima? Ta hanyar ilimi, da kuma goayya da na gaba, waɗanda suka san rayuwa. Iya ilininka, iya hikimarka! Shi ya sa ba son ɗan Adam ya dena neman ilimi. Saboda ilimi yana da tasiri ga hankali, da hikima, da azancin ƙwaƙwalwa.
  6. Adani: ita ƙwaƙwalwar ɗan Adam, duk yadda za ta yi, za ta yi domin ɗan Adam ya ci gaba da rayuwa . Shi ya sa take taskance bayanai na yadda ake yin abubuwa saboda da zarar ɗan Adam ya buƙaci yin wani abu, to sai dai kawai ta bude wannan taska ko “memory”  ta ɗauko abinda ake buƙata.  Idan mutum ya koyi tuƙin mota, to ba ruwansa da ya sake koya; idan mutum ya koyi magana ko tafiya, to ba ruwansa da ya sake koya,  matuƙar bai samu wata matsala ta haɗari ko gogewar taskar bayanai a ƙwaƙwalwar tasa ba. Adana bayanai masu alaƙa da abubuwan da muke yi kullum a rayuwarmu, shi ke sa ƙwanwalwa ta samar da ɗabi’a.  Amfanin ɗabi’a shine gudanar da ayyukanka ko ayyukanki na yau da kullum cikin sauƙi ba tare da kin tsaya tantama ko shakka ba; irin ki ce :” Ya ma ake shara?”, ko “ya ma ake wanke-wanke.”

Ni yanzu idan zanyi rubutu, wasu lokutan nakan kawar da kaina kuma ina rubutun cikin salula ta, ba tare da na kalli madannan wayar ba. Me yasa? Saboda hakan ya zama jiki, an taskance bayanan yadda zanyi na rubuta “ruwa” ko “Mustapha” a cikin ƙwaƙwalwa ta. Da fatan an gane.

Masu karatu mu haɗu a rubutu na gaba domin jin yadda sauran bayanin zai kaya.

Comments

Popular posts from this blog

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da y...

SUNAYEN HAUSAWA DA MA'ANONINSU.KASHI NA DAYA.

TANKO: Yaron da aka haifa bayan mata. KANDE: Yarinyar da aka haifa bayan maza. KILISHI: Yarinyar da aka fara haifa babanta ya samu sarauta. BARAU: Yaron da aka haifa ya rayu, amma an haifa wasu kafin shi ba su rayu ba. SAMBO: Yaron da aka haifa bayan maza da yawa. TALLE: Yaron/yarinya da mahaifiya ta rasu tana gama haihuwa. AUDI: Yaron/yarinyar da mahaifi ya rasu kafin a haife. MIJIN-YAWA: Yaron da aka haifa dukkanin kakannin sa suna raye. DIKKO: Yaron da aka fara haifa (Dan fari). SHEKARAU: Yaron da ya shekara a ciki MAIWADA: Yaron da aka haifa iyaye suna cikin wadata. GAMBO: Yaron/yarinyar da aka haifa bayan tagwaye. CINDO: Yaron/yarinyar da aka haifa da yatsu shida. MARKA: Yarinyar da aka haifa lokacin marka-marka. ALHAJI: Yaron da aka haifa lokacin aikin haji. AZUMI: Yaron/yarinyar da aka haifa lokacin azumi. SARKI: Yaron da aka sama sunan sarki. SUNAYEN NA’URORIN BATURE DA AKA CANZA MASU SUNA ZUWA HAUSA. Ford = Hodi Bedford = Bilhodi Mercedes = Marsandi Peugeot = Fijo Volkswagen =...

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All...