WATAN SHA'ABAN:
SALLOLIN DARAREN
SHA'ABAN:
DAREN FARKO:
An karbo daga Manzon (S) ya ce: "Wanda ya yi sallah a daren farko na Sha'aban raka'a (12) a kowace raka'a ya karanta Fatiha (1) Kulhuwa (15) Allah zai rubuta masa ladar ibadar shekara goma sha biyu. kuma za a gafarta masa zunubbansa kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi" (Dhiya'us Saliheen.29).
SALLAH TA BIYU:
Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa(30) Idan an sallame a ce: Allahummah Haaza Ahdiy Indaka Ila Yaumil Kiyamah".Wanda ya yi wannan sallah. Allah zai kare shi daga tarkon shedan da rundunarsa. kuma ya ba shi ladar Salihan bayi. (Dhiya'u.29).
SALLAH TA UKU:
Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (11) Wanda ya wannan sallah. Allah zai tsre shi daga sharrin halittun sammai da na kassai. kuma zai gafarta masa zunubbai Subu Saba'in na kaba'irah da ke tsakaninsa da shi Allah.
DARE NA BIYU:
Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (11) Wanda ya yi wannan sallah. Allah zai tsare shi daga sharrin halittun sammai da na kassai. kuma zai gafarta masa zunubbai Dubu saba'in na kaba'irah da ke tsakaninsa da shi Allah.
SALLAH TA BIYU:
Sallah raka'a (50) a kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (1) Falaki (1) Nasi (1) Allah zai sa Mala'iku su daina rubuta masa zunubi na tsawon shekarar.
DARE NA UKU:
Sallah raka'a (2) kowace raka'a a karanta Fatiha (1) Kulhuwa (11) Wanda ya yi wannan sallah Allah zai gafarta masa zunubin kaba'ira (70) kuma ya tunkude masa azabar kabari.
SALLAH TA BIYU:
Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (25) Allah zai bude wa wanda ya ui wannan sallah kofofin Aljanna ya rufe masa na wuta.
ADDU'A:
Da asubahin daren uku ga watan Sha'aban ne aka haifi Imam Hussain (AS) dan haka ana son karanta addu'ar nan ta 'As'aluka Bihakkil Mauludi Fiy Hazhal Yaumi' da ke shafi na (33) a 'Dhiya'us Saliheen'. ko shafi na 261 a 'Mafateehul Jinan' don Tawassuli da Imam Hussain (AS) ga samin biyan bukatu.
DARE NA HUDU:
Sallah raka'a (40) a kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (25) Allah zai rubuta wa wanda ya yi wannan sallah ladar shahidai (1000)
DARE NAa BIYAR:
Sallah raka'a (2) a kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (150) bayan an yi sallama sai a yi Salatin Annabi (70) Allah zai biyawa mutum bukatu dubu a duniya da lahira.
SALLAH TA BIYU:
Manzon Allah (S) ya ce: "Wanda ya yi Sallah raka'a (2) a daren biyar (na Sha'aban) Ya karanta Fatiha (1) Kulhuwa (500) Wato kowace Raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (250) bayan ya sallame ya yi Salatin Annabi kafa (70) Allah zai biya masa bukatu Dubu a duniya da lahira" (Baladul-Ameen.shafi na 181)
DARE NA SHIDA:
Sallah raka'a (4) kowace raka'a Fatiha (1) Kulhuwa (50) Wanda ya yi wannan Sallah Allah zai rabautar da shi. ya kuma yalwata masa kabari.
DARE NA BAKWAI:
Sallah raka'a (2) a raka'ar farko Fatiha (1) Kulhuwa (100) A raka'ar ta biyu. Fatiha (1) Kursiyyu (100) Wanda ya yi wannan Sallah to zai zamo a cikin Muminai.
SALLAH TA BIYU:
Manzon Allah (S) ya ce: "Wanda ya yi sallah raka'a biyu (a dareb 7 na Sha'aban) a raka'ar farko ya karanta Fatiha (1) Kulhuwa (100) A raka'a ta biyu Fatiha (1) Kursiyyu (1) Allah zai amsa addu'arsa. ya biya masa bukatunsa. Kuma a kowace rana (ta watan) za a rubota masa ladar Shahidi" (Baladul Ameen.182).
DARE NA TAKWAS:
Sallah raka'a (2) Raka'ar farko Fatiha (1) Amanar-Rasulu zuwa karshen sura sau (5) sai Kulhuwa (15) A raka'a ta (2) Fatiha (1) ayar karshe ta suratul kahfi (1) sai Kulhuwa (15) Allah zai gafartawa Wanda ya yi wannan sallah duk laifukansa.
DARE NA TARA:
Sallah raka'a (4) a kowace raka'a Fatiha (1) Izaja'a (10) Wanda ya yi wannan Sallah Allah zai haramta namansa daga wuta. ya ba shi ladan shahidai (12)
DARE NA GOMA:
Sallah raka'a (4) a kowace raka'a Fatiha (1) da Ayatal Kursiyyu (1) Inna A'adaina (3) Wanda ya yi wannan sallah Allah zai rubuta masa kyawawan aiki dubu Dari.
DARE NA SHA-DAYA:
Sallah raka'a (8) a kowace raka'a Fatiha(1) Kuliya (10) Wanda ya yi wannan Sallah. Allah zai ba shi a kowacce raka'a dausayi a Aljannah.
DARE NA SHA BIYU:
Sallah raka'a (12) kowace raka'a Fatiha (1) Alhakumu (10) wanda ya yi wannan Sallah. Allah zai ba shi ladar bauta a daren Lailatul kadari.
DARE NA SHA UKU:
Sallah raka'a (2) a kowace raka'a Fatiha (1) Watteeni (1) Allah zai gafarta wa mutum zunubbansa baki daya
SALLAH TA BIYU:
Sallah raka'a (2) kowace raka'a Fatiha (1) Yaseen (1) Tabara (1) Kulhuwa (1) Wanda ya yi wannan sallah. Allah zai azurta shi da boyayyun sirruka na falalar da ke cikin watannin nan guda uku (wato Rajab. Sha'aban. Ramadan) kuma Allah zai gafarta masa dukkan zunubbansa muddin ba shirka ba ne" (Ikbal fil A'amal)
DARE NA SHA HUDU:
Sallah Raka'a (4) a kowace raka'a Fatiha (1) Wal'asri (5) Wanda ya yi wannan Sallah Allah zai rubuta masa ladar masu sallah tun daga Adamu (AS) har ranar karshe.
SALLAH TA BIYU:
Sallah raka'a (4) kowace raka'a Fatiha (1) Yaseen (1) Tabara(1) Kulhuwa (1) Wanda ya yi wannan sallah. Allah zai azurta shi da boyayyun sirruka na falalar da ke ciki watannin nan guda uku (wato Rajab. Sha'aban. Ramadan) ku ma Allah zai gafarta masa dukkan zunubbansa muddin ba shirka ba ne.
Daga
SANI ABUBAKAR DIKUWA.
Comments
Post a Comment