Skip to main content

Posts

START YOUR FISH FARMING❓

SANI ABUBAKAR DIKUWA IN A FARM. Contents Chapter 1 Introduction   Chapter 10 Taking Care of your Pond Chapter 2 Locating your Fish Farm   Chapter 11 Taking Care of your Fish Chapter 3 Constructing Fish Ponds   Chapter 12 Harvesting your Pond Chapter 4 Inlets to Let Water into the Pond   Chapter 13 Beginning Again Chapter 5 Outlets to Let Water Out of the Pond   Chapter 14 Improving Farm Management Chapter 6 Bringing Water to your Ponds   Chapter 15 Producing Fish in Pens Chapter 7 Controlling the Water in the Pond   Chapter 16 Producing Fish in Cages Chapter 8 Preparing your Pond   Chapter 17 Your Farm and your Fish Ponds Chapter 9 Stocking your Pond with Baby Fish   Chapter 18 Keeping you and your Family Healthy     Test your Knowledge     1. INTRODUCTION   What is fish farming? Why do we raise fish? What do you need to raise fish? How do we begin? 2. LOCATING YOUR FISH FARM   Where to put your fish pond Water s...

NOMAN KIFI

  Yadda ake fara noman kifi A gaskiya ma, bayanin kyau ya bambanta daga mutum zuwa mutum. Duk da haka, idan aka ambaci kwayoyin ruwa musamman kifaye a cikin tafki mai kyau, kowa yana ganin su suna da ban sha'awa. Duk da yake yana iya yin sauti duka hadaddun zuwa raya kifin, a nan, za mu ɗauke ku wannan tsari mataki-mataki don tabbatar da cewa ba kawai kayan aiki ne kawai ba amma har ma da kuzarin fara noman kifi. Cike da sha'awa, goyan bayan gwaninta, muna juyar da duk ra'ayoyinku da zaburarwa zuwa ga nasara mai ban sha'awa. Menene noman kifi? Mahimmanci, noman kifin da aka fi sani da pisciculture tsarin ciyar da halittun da ke zaune a cikin ruwa na kasuwanci ko dai a cikin yanayi mai sarrafawa ko kuma ba a sarrafa shi ba don ƙara yawan aiki. Yadda ake fara noman kifi mataki-mataki Kifin kifin tsari ne sosai. Kamar yadda aka ambata a baya, muna ɗaukar ku da gwaninta tun daga lokacin da kuka zaɓi wurin da kuke son adana kifi har zuwa mataki na ƙarshe inda zaku tallata sh...

MAGANIN CIWON CIKI NA BANGAREN HANUN HAGU.

*DAGA ZAUREN SASHIN BASIRA* Mene maganin ciwon ciki na barin hannun hagu❓   🤔Ciwon ciki na bangaren hagu yawanci yana faruwa ne daga hanji ga mata kuma yafi faruwa ne saboda hannun mahaifa na hagu idan ciwon bai yawa ba yana tafiya dakansa cikin kwana 1-2,amma idan ciwon yazo da zazzabi, Ciwon yayi yawa ko wurin ya kumbura, ko kashin jini, ko yawan tashin zuciya ko amai, ramewa, ko fatar tazama yellow to akwai bukatar zuwa asibiti.  🔸 *Diverticulitis* yana yawan kawo irin wannan musamman mutanen da suka kai shekara 40 zuwa sama, diverticulis wasu yan jikkuna ne ke samuwa akan hanji to idan suka kece ko suka kumbura ko infection yashiga sai diverticulis din yafaru yana zuwa da zazzabi, tashin zuciya, amai, kumburin ciki. Idan wannan ne yawanci Idan aka chanza abinci akasamu hutu sosai da wasu yan antibiotics anasamun lafiya 🔸 *Gas,* shima yana kawo ciwon ciki na bangaren hagu saboda idan gas yashiga cikin hanyoyin ko bututun narkarda abinci zuwa hanjin takashi inda daga nan ...

TARIHIN ZAGAYOWAR SHEKARAR MUSULUNCI.

Assalamu alaikum. Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci. Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne. Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba. Masu wannan fahimtar Malamai sun ce ba wai suna nufin a koma wa Sunnar Manzon Allah ba ne, suna so ne a koma wa zamanin Annabi (SAW), ka ge ke nan sai mu ajiye su motoci da sauran kayan kere-kere na fasaha sda ake amfani da su yanzu har da su lantarki da su jirgin sama duk a ajiye, a koma amfani da su rakuma da dawaki da jakuna. Idan kayan yaki ne ma a ajiye su nukiliya, da manyan tankokin yaki da su jiragen yaki sai dai a yi amfani da su kwari da baka da takubba, idan an tari abokan gaba da wadannan an yi bidi’a kamar yadda fahimtar wadancan mutanen take. Ka ga idan aka yi haka ai hankali ya warware. Kur’anin da Allah ya saukar mana zamaninsa ba ya shudewa, ya dace da kowane irin zamani da ya zo, ko zai z...

SHIN AURE NASARACE, KO RASHIN NASARA A RAYUWA.

Shin aure nasara ce ga mutane? -  amarya Me kake so? Ya za ka yi ka same shi? Ka samu? "Marriage is not an Achievement" Aure ba shi ne ci gaba ba ko ba shi ke nuna nasara ba. Wannan ne batun da ya tayar da ƙura a kafafen sada zumunta a wasu watanni da suka gabata, a kwanan nan ma an sake tayar da ƙurar a kafar sada zumunta ta tuwita. Mutane da dama suna bayyana ra'ayoyinsu da fahimtarsu game da batun, wasu na ganin aure shi ne nasarar rayuwa yayin da wasu ke ganin cewa ba shi ne nasarar rayuwa ba. An yi ta ba da hujjoji na ilmi da kuma na ra'ayoyi akai, daidai da yadda ko wanne mutum ya fahimci rayuwa ko kuma fassarar da ya yi wa samun nasara. Wannan ce-ce-ku-ce ya taimaka ƙwarai wajen bayyana mana cewa ko wanne mutum akwai ma'anar da ya bai wa nasara da abin da yake ganin idan ya mallaka ya sami nasara. Rayuwar ko wanne mutum cike take da burika manya da ƙanana. Ɗan adam kan share doguwar tafiya wajen neman cika manyan burikansa, yayin da yake ta koka...

ABUBUWA (9) DA YA KAMATA MUSULMAI SU YI A WATAN DHUL AL-HIJJAH.

Annabi muhammad (SAWA) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanakin goman farkon watan Dhu al-Hijjah Malamai na ci gaba da fadakar da al'ummar Musulmi dangane da falalar kwanaki goman farko na watan Dhul Hijjah, Musulmi dai na daukar kwanaki goman farko na wannan watan a matsayin mafi daraja a wajen Allah. Hadisi ya zo cewa Annabi Muhammad (SAW) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanaki goman farkon watan Dhu al-Hijjah. Akwai kuma ibadu da ɗabi'u da Musulmi ke siffantuwa da su a cikin wadannan ranakun da suka haɗa da yin azumi da hawan Arfa da kuma layya domin neman kusanci ga Allah Ubangiji. Sheikh Sani yahaya Daban-fulani, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya ya yi wa mana bayani kan muhimmancin watan na Dhu al-Hijjah da kuma abubuwan da ya kamata Musulmi suyi KADA A ASKE GASHI, DA YANKE FARCE Abu na farko shi ne idan mumutum yana da niyyar zai yi layya, to daga daya ga watan Dhu al-Hijjah kada ya yank...

KUDIN RUWA NA BANKI RIBACE???

Na lura cewa a duk inda Musulmi su ke a fadin duniya, ana samun irin wannan matsala kuma ya jawo koma bayan tattalin arzikin Musulmi. Wannan dalili ne ya sa na shiga bincike game da yadda riba ta ke a hakika a Musulunci. Abinda ya fara bani mamaki shine na gano cewa babu wata matsala wadda ta dade ta na ciwa Musulmi tuwo a kwarya irin maganar riba domin ta faro ne tun zamanin sahabbai. Annobar Kwarona ta jefa miliyoyin mutane a Arewacin Najeriya cikin wannan tsaka me wuya sakamakon samun hanyoyin karbar basuka musamman wanda Babban Bankin kasa ya fito da shi na tallafawa mutane da kananan sana’o’i. Amma waccan Magana ta riba na yin tarnaki ga mutane da dama. Akwai wani matashi an bashi bashin miliyan hudu amma mahaifiyarsa ta hana shi karba, sannan wani abokina ya sami damar karbar bashi na kimanin miliyan 238 amma malamai sun hana shi, saboda dalilai na riba. Abu na farko da ya kamata mu fara fahimta game da riba shine abinda malamai ke kira da Asbabul Nuzul, wato dalilin saukar aya. ...