Skip to main content

MAGANIN CIWON CIKI NA BANGAREN HANUN HAGU.


*DAGA ZAUREN SASHIN BASIRA* Mene maganin ciwon ciki na barin hannun hagu❓
  🤔Ciwon ciki na bangaren hagu yawanci yana faruwa ne daga hanji ga mata kuma yafi faruwa ne saboda hannun mahaifa na hagu idan ciwon bai yawa ba yana tafiya dakansa cikin kwana 1-2,amma idan ciwon yazo da zazzabi, Ciwon yayi yawa ko wurin ya kumbura, ko kashin jini, ko yawan tashin zuciya ko amai, ramewa, ko fatar tazama yellow to akwai bukatar zuwa asibiti.
 ðŸ”¸ *Diverticulitis* yana yawan kawo irin wannan musamman mutanen da suka kai shekara 40 zuwa sama, diverticulis wasu yan jikkuna ne ke samuwa akan hanji to idan suka kece ko suka kumbura ko infection yashiga sai diverticulis din yafaru yana zuwa da zazzabi, tashin zuciya, amai, kumburin ciki. Idan wannan ne yawanci Idan aka chanza abinci akasamu hutu sosai da wasu yan antibiotics anasamun lafiya
🔸 *Gas,* shima yana kawo ciwon ciki na bangaren hagu saboda idan gas yashiga cikin hanyoyin ko bututun narkarda abinci zuwa hanjin takashi inda daga nan sai bayan gida saiya haifarda kumburin ciki da marsalar narkewar abinci. Yana zuwa da ciwon cikin bangaren hagu, gudawa, amai, kashin jini, bugun zuciya, ramewa. Shikuma cin abinci dayawa, yawan hadiyar iska yayin hadiyar abinci, chin chingum, cin abinci ko shan abu mai gas, kokuma chin abinci dasuke da wuyar narkewa duk suna kawo shi.
 ðŸ”¸ *Indigestion,* rashin narkewar abinci nakawo irin wannan ciwon cikin na hagu, yana zuwa da kumburin ciki, yawan tusa, tashin zuciya, ciwon zuciya.
 ðŸ”¸ *Hernia, kidney stones, shingles,* duk suna kawo shi
👩‍👩‍👦‍👦Amma ga mata kawai akwai endometriosis, karin hannun uwa, ciwon al'ada, chanza wuri da hannuwa mahaifa keyi, ciki na wajen mahaifa, pelvic inflammatory disease.
👨‍👨‍👦‍👦 Amma ga maza kawai, hernia, chanza wuri na maraina
 Kaga treatment dole sai angane miye yakawo shi idan kuma yazo ne kawai cikin kwana daya zuwa biyu yatafi kuma bawani ciwo bane dayawa kuma ba wadancan alamun to ba damuwa.
 *DAGA SANI ABUBAKAR DIKUWA*                     Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinnan 
saniabubakardikuwa7@gmail.com 

Comments

Popular posts from this blog

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da y...

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All...

ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM KASHI NA BIYU

 Æ˜waÆ™walwar É—an’adam (2) DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin É—an adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin. A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa Æ™waÆ™walwar É—an Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda Æ™waÆ™walwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. ƘwaÆ™walwar mutum guda É—aya ce amma tana da É“angarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin Æ™oÆ™on kai, da kuma wadda ke Æ™asan Æ™eya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take Æ™asanta, wadda ta haÉ—e da laaka dake gadon bayan mutum. Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin Æ™oÆ™on kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta É“ari biyu ce: É“arin hagu da É“arin dama. Wasu masanan sun ce aikin da Æ™waÆ™walwar dama ta ke yi...