Skip to main content

ABUBUWA (9) DA YA KAMATA MUSULMAI SU YI A WATAN DHUL AL-HIJJAH.

Annabi muhammad (SAWA) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanakin goman farkon watan Dhu al-Hijjah
Malamai na ci gaba da fadakar da al'ummar Musulmi dangane da falalar kwanaki goman farko na watan Dhul Hijjah,

Musulmi dai na daukar kwanaki goman farko na wannan watan a matsayin mafi daraja a wajen Allah.

Hadisi ya zo cewa Annabi Muhammad (SAW) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanaki goman farkon watan Dhu al-Hijjah.

Akwai kuma ibadu da ɗabi'u da Musulmi ke siffantuwa da su a cikin wadannan ranakun da suka haɗa da yin azumi da hawan Arfa da kuma layya domin neman kusanci ga Allah Ubangiji.

Sheikh Sani yahaya Daban-fulani, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya ya yi wa mana bayani kan muhimmancin watan na Dhu al-Hijjah da kuma abubuwan da ya kamata Musulmi suyi

KADA A ASKE GASHI, DA YANKE FARCE

Abu na farko shi ne idan mumutum yana da niyyar zai yi layya, to daga daya ga watan Dhu al-Hijjah kada ya yanke farce kuma kada ya aske gashin jikinsa. Domin Allah (SWA) zai ba shi lada adadin yawan gashin kansa da kuma adadin tsawon faratansa har ya zuwa lokacin da zai yi layyarsa. Daga nan kuma sai ya je ya yi aski da yanke faratan nasa.

AZUMIN RANAR ARFAT.

A cewar Sheikh Sani yahaya Daban-fulani, abu na biyu shi ne, ana so mutum ya yi azumin ranar Arfa. Hadisi ya zo cewa azumin ranar Arfa yana kankare zunubin shekarar da ta gabata da kuma wacce za ta zo.

LAYYA.

Abu na uku shi ne ana so mutum ya yi layya. Yin layya koyi ne da Sunnar Annabi Ibrahim (ASW), wanda Allah ya umarce shi ya yanka dansa domin ya jarraba shi, ya ci jarrabawar har aka fanshi dan nasa da rago.

Manzon Allah ya sayi raguna guda biyu ya yanke, sannan ya ce duk wanda yake da hali ya yi layya.


Ana so kuma mutum ya yi sallar Idi ranar ta Idi, kuma ya yi kwalliya da sabbin tufafi. Idan ba shi da sabbi ya sanya mafiya kyawu da yake da su. Ana bukata kuma ya kyautata wa iyalinsa, su ma ya saya musu sabbin tufafi idan da hali. Kazalika su fita a je sallar idi tare da mata.

AZUMIN WATAN DHUL AL-HIJJAH.

Baya ga azumin ranar Arfa, ana so mutum ya yi azumi a wasu daga cikin ranakun watan na Dhu al-Hijjah tun daga farkonsa. Zai iya yin hakan ko da kuwa ana bi sa azumin watan Ramalana.

YAWAITA SADAKA.

Akwai matukar muhimmanci mutum ya yawaita sadaka a watan Dhu al-Hijjah; misali, idan yana sadakar N1000, to ya kamata ya kara zuwa sama da haka, ko ma ya nunka idan yana da hali.

Wani karin abu shi ne, mutanen da ba za su je aikin Hajjin bana ba, za su iya amfani da wani kaso na kudinsu wajen sayen kayan abinci da tufafi su bai wa marasa karbi. Shi ma aikin sadaka 

SADA ZUMUNTA.

Ana so Musulmi ya dage wajen yin zumunci da kai ziyara ga 'yan uwa da abokan arzuki a wannan watan

Haka kuma ana so mutum ya yawaitar kabbar a wannan wata mai albarka. Yana da kyau a yi kabbarori nau'i daban-daban irin su Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha illalLah Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamdu

HAJJI.

Sannan ana so a wadannan kwanaki mutum ya je ya yi aikin Hajji ko Umrah.

Malamai sun ce wadannan ayyuka na ibada sun hade kusan dukkan rukunan Musulunci, shi ya sa ake kwadaitawa Musulmi su juri yinsu a wannan wata mai alfarma.

Comments

Popular posts from this blog

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da y...

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All...

ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM KASHI NA BIYU

 Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2) DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin. A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin ƙoƙon kai, da kuma wadda ke ƙasan ƙeya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take ƙasanta, wadda ta haɗe da laaka dake gadon bayan mutum. Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin ƙoƙon kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta ɓari biyu ce: ɓarin hagu da ɓarin dama. Wasu masanan sun ce aikin da ƙwaƙwalwar dama ta ke yi...