Shin aure nasara ce ga mutane? -
amarya
Me kake so? Ya za ka yi ka same shi? Ka samu?
"Marriage is not an Achievement" Aure ba shi ne ci gaba ba ko ba shi ke nuna nasara ba. Wannan ne batun da ya tayar da ƙura a kafafen sada zumunta a wasu watanni da suka gabata, a kwanan nan ma an sake tayar da ƙurar a kafar sada zumunta ta tuwita.
Mutane da dama suna bayyana ra'ayoyinsu da fahimtarsu game da batun, wasu na ganin aure shi ne nasarar rayuwa yayin da wasu ke ganin cewa ba shi ne nasarar rayuwa ba.
An yi ta ba da hujjoji na ilmi da kuma na ra'ayoyi akai, daidai da yadda ko wanne mutum ya fahimci rayuwa ko kuma fassarar da ya yi wa samun nasara.
Wannan ce-ce-ku-ce ya taimaka ƙwarai wajen bayyana mana cewa ko wanne mutum akwai ma'anar da ya bai wa nasara da abin da yake ganin idan ya mallaka ya sami nasara.
Rayuwar ko wanne mutum cike take da burika manya da ƙanana. Ɗan adam kan share doguwar tafiya wajen neman cika manyan burikansa, yayin da yake ta kokawar rayuwa da ƙananan burika, yana samun nasara akan wasu, wasu kuma suna kubucewa.
Ana samun bambance-bambancen burika daga wannan mutum zuwa wancan, abin da wancan yake so ba shi wannan yake so ba, haka ma kuma bin hanyar cika burikan, wani ya kan zo masa da sauki wani kuma da tsanani, sannan a karshe wani yana zamun nasara wani kuma yana rasawa.
Hatta mutanen da ke da buri iri daya, idan aka bincika sosai, za a fahimci cewa hanyar da suke bi domin cimma burinsu ta sha banban da juna.
Shi ya sa masana suka sha fadar cewa babu wata takamaimiyar hanyar nasara (formula) a rayuwa, domin hanyar da wani ya bi ta bille masa wani idan ya bi, bata zai yi.
Duk wasu burika da fata manya da kanana da dan adam ya cimma don amfanar da kai ko al'umma ko ma duniya gabadaya, duk ana kiran wannan da "Achievement" a turance. Ma'ana Nasara kenan ko kuma cimma wani buri da aka sa a gaba.
Yanzu tambayi kanka, Me kake so? Ya zaka yi ka same shi? Ka same shi? Idan ka same shi, to ka yi nasara "achieving", idan kuma ba ka yi nasara ba, to kai tsaye a iya cewa ba ka yi "achieving" ba.
Aure nasara ko rashin nasara
Game da wannan batu na cewa Aure shi ne Nasara" a bisa shimfidar da mu ka yi wajen bayyana menene nasara, "Achievement" sai mu ga cewa kenan dukkan mutane ba za su iya taruwa su yanke hukuncin cewa aure shi ne nasarar rayuwa ba, ko kuma su yanke kaunar cewa ba shi ne nasarar ba, saboda bambance-bambancen kudurori da fatan da 'yan adam ke da su, yayin da wancan yake son aure wancan so yake ya zama hamshakin dan kasuwa, yayin da wancan ke son zama malamin jami'a, wancan so yake ya zama lauya.
Idan ka so aure sannan kuma ka samu to ka yi "achieving", idan ka so zama lauya shi ma ka samu ka zama kai ma ka yi achieving, idan ma so kake ka yi rayuwarka haka ba tare da aure ba, kuma ka samu ka yi zamanka hakan lafiya lau ba tare da kauce hanya ba, to nan ma ka yi achieving wato ka sami nasara a abinda ka ke so.
Sannan idan ma duk za mu taru mu kalli aure a mahanga guda, wato aure shi ne nasarar rayuwa musamman idan mun yi la'akari da hujjojin da wasu ke bayarwa cewa ta hanyar aure ake samar da dan adam, amma dai dukkanmu mun san cewa ta hanyar haihuwa ake samun dan adam, kasancewar akwai milyoyin mutanen da aka haifa ba tare da aure ba.
Sai dai aure kyakkyawan aiki ne da yawancin addinai da al'adu suka gamsu da shi, don ta hanyarsa a kan taskance iyali da nasaba.
Sannan muhimmiyar bauta ce da addinin musulunci ya shar'anta wadda kuma ake samun gwaggwaɓan lada ga wadanda suka cika sharuɗɗa da dokokin da addinin ya gindaya a auren, sannan akan iya samun zunubi ga wanda ya yi fatali da dokokin.
A nan gaɓar ma abinda za mu gane shi ne, ko iyakar nasarar kowa ta ta'allaka a aure ne, to dole wasu ma'auratan sun yi nasara wasu kuma sun fadi.
Tun daga kan zabin abokin zama, idan ka samu irin wanda kake so lallai ka yi nasara, idan kai da abokin zamanka kuka zauna lafiya kowa yana biyan hakkin dan uwansa duk kun yi nasara, idan kuka samu zuriya ku ka sauke hakkinsu sannan kuka ba su tarbiya irin ta addinin Musulunci kun yi nasara.
Idan burinka ka auri mata hudu rigis! kuma zuka-zuka, sannan ka samu ka aura din, ka yi nasara, idan ka yi burin auren wata mahadacciyar Alkur'ani, kuma ka yi katari ka samu ka aura, ka yi nasara.
Idan kika yi burin auren hamshaƙin mai kudi, kuma kika samu kika aura, kin yi nasara, idan kika yi burin auren wani Ustazu kuma kika samu nasarar aurensa, ke ma kin yi nasara!
Amma ya lissafin zai kasance idan mun kalli bangaren akasin haka fa? Ma'auratan da suka kasa zaman lafiya a tsakaninsu suka kare rayuwarsu cikin zaluntar juna sun yi nasara kenan?
Da muguwar rawa gwamma ƙin tashi
Gwamnati ta sha yi wa zawarawa aure a Kano don magance mace-macen aure
Ma'auratan da suka kasa sauke hakkin junansu da addini ya rataya musu, sun yi nasara kenan? Ma'auratan da suka haifi 'ya'ya suka kasa sauke hakkinsu na daukar nauyi da tarbiya suka bar su suka zama 'yan iskan gari su ma wadannan sun yi nasara kenan?
An sha samun miji ya kashe matarsa ko mata ta kashe mijinta, su ma wadannan sun yi nasara kenan? idan dai ana danganta nasara da abinda yake me kyau amsar ita ce wadannan ba su yi nasara ba.
Ta fuskoki da yawa akwai aurarrakin da rashin yin su ya fi yin su amfani.
Ta fuskar addini duk auren da zunubi zai kwasa maimakon lada, rashin yin sa ya fi yin sa amfani, duk auren da zai haifar da al'umma marasa manufa kuma zai janyo gurbacewar tarbiya, rashinsa ya fi yin sa amfani.
Bayan waɗannan kaso biyu na masu nasara da masu faduwa a tare, akwai kason karshe wanda daya ke nasara dayan kuma ya fadi.
Mijin da ya yi nasarar samun irin matar da yakeso, amma matar ba ta yi dacen samun irin mijin da take so ba, ko kuma matar ta samu mijin da take so, shi kuma bai samu irin wadda yake so ba.
Ko ɗaya ya kyautata daya kuma ya muzguna, to wadannan idan an tashi warewa dole a ce daya ne ya yi nasara daya ya fadi.
Na san wani zai amsa min da cewa duk maganganun nan kan ma'aurata ake ba aure ba, ai shi aure yana nan a matsayinsa na aure wanda ba zai canja shi saboda gurbacewar ma'aurata ba.
To dama maganarmu na magana ne kan ma'auratan wadanda su ake tambaya sun sami nasara a aurensu ko sun gaza?
Ko da yake a farkon maganarmu mun kawo batun kowa da abinda yake kallo a matsayin nasara.
Daga karshe. Albishirinku! Abubuwan da kuke bukatar nasara a kansu suna da yawa, ku mayar da hankali ku cimma su duka, sai ku zama me nasarar nasorori.
Watakila cikin abubuawan da kuke bukatar nasara a kansu, har da hadiye fushinku duk lokacin da ra'ayi ko fahimtar wasu ta saba da taka ko?
Kuma ku dade kuna tuna wa kanka kuna bukatar amfani da hankali maimakon amfani da karfi a lokacin da za ka yi magana bayan ka gama sauraron ra'ayi ko fahimtar da ta saba da taka ko?
Kuma kuna son ka fahimtar da me wancan ra'ayin irin naka ra'ayin? Haka ne? Babu wahala, fara kwatantawa daga yanzu. Idan kuka yi nasarar gyara kanka, shi ne babban ''achievement'', wato nasara.
Bissalam
SANI ABUBAKAR DIKUWA
Comments
Post a Comment