A wata yanayi dake dauke hankali a duniya, tare da barazana da cecekuce dake da ake yi tsakanin manyan kasashe irin su Koriya ta Arewa da kasar Iran ko Farisa, da kuma Amurka a yau. Daga cikin manyan abubuwa da ke sawa hakan akwai shirinsu na mallakar wani makamin tsare kasa da ake kira makamin Nukiliya, ko kuma (Nuclear Weapons) a harshen Turanci.
Ita dai Nukiliyya, ta samo asali ne daga Italiya. Nukiliya na da fannoni daban-daban, kamar samar da wutar lantarki, zaman takewar gida, da sauran su. Har ila yau Nukiliyya na da fannin makami wanda shine maudu’in da zamuyi bayani akai.
Makamin Nukiliiya zai ita zama Bom din Atom, ko Bom din Nukiliya, makami ne mai karfin gaske da saurin fashewa saboda sinadarin kayan kimiya dake dauke dashi masu tarwatsewa, ko harhadewa da junan su don haifar da makamashin Madda (Antomic Energy) a yanayin feso hayaki ko da haske mai dauke da Guba ga lafiya ko rayuwar Dan Adam da muhallin sa.
Idan makamin Nukiliya ya fashe a wuri ko gari, Misali, dole a ji fashewa mai tsananin karar gaske mai firgitarwa, tare da cutarwa ga rayuwar Dan Adam ko sauran halittu masu rai, saboda hayakin da yak e fitar wa mai Guba, da wutar mai ci bal-bal, a karshe tare da tiririn hayaki mai cutarwa da ke biye dashi, wanda idan ya sauka a wuri ya na iya bata dukkannin ilahiran wajen na tsawon shekaru. Duk wajen da Makamin ya sauka, zasu rasa abubuwa kamar; Iska mai dadi, kuma zaman wurin bazai yi dadi ba, komai na wajen zai gurbace saboda saukar Makamin Nukiliya.
Idan mizanin makamin da aka harbo ya kai karfin Tan Miliyan Daya (1 million ton), to karfin fashewar sa na iya haddasa ‘yar karamar girgizan kasa na ‘yan takaitattun taku daga wajen da fashewar ya auku. Haka zalika, makamin Nukiliya, nada shahararru nau’uka iri biyu, wanda dukkan sauran nau’ukan suna karkashin biyun ne. Na farko, shine nau’in da ke dauke da makamshin Madda mai karfi, masu tarwatsa junan su ta hanyar warwatsewa, da suke yayin da aka harba su ta hanyar makamin da suke dauke a cikin sa. Akan jera wayan nan makamai masu gaggawar fashewa ne waje daya, sannan a harba su inda ake hari. Wannan tsarin kenan wanda ake kira da (Gun Method).
Dayan kuma wato nau’i na 2, wanda ake kira da Fulotoniyon (Implosion Method) a wuri daya, Suna harhadewa waje daya yayinda aka harba su, kuma suna kunshe ne da nau’in farko na Nukiliyan, mai suna Bom din Atomik (Atomic Bomb) a harshen Turanci. Da irin wannan Nau’in ne kasar Amurka ta jefa wa kasar Jafan a manyan Biranen su, lokacin yakin Duniya ta 2 (World War 2) wanda ya auku a shekara ta 1945.
Sai wani Nau’i wanda ke kunshe da makamashin Guba mai yawan gaske saboda yawan sinadarai na Madda masu tarwatsewa, da kuma Madda masu hadewa kafin fashewa. Da zarar makami mai dauke da wannan kunshin ya sauka inda ake hari, sai wadannan sinadaren su tarwatsewa cikin ma’adanar, Kuma zai iya haifar da haske mai nau’in na (Gamma Ray) da kuma (D-Ray) wanda ke narkar da sinadaran da Nukiliyan ke dauke dashi. Wannan Nau’in shi ake kira da Makami mai Guba (Hydrogen Bomb), ko (H Bomb) a harshen turanci.
A tarihin Duniya, sau 2 kacal aka taba anfani da Nukiliya, a wurare 2, sannan a kasa 1, a lokacin yakin Duniya ta 2, wanda ya auku a shekara ta 1945. Wanda aka kai harin kasa da kasa. Wanda kasar Amurka ta harba wa kasar Jafan, wata makamin Nukiliya mai dauke da nau’in makamshin Yuraniyom, (Uranion) mai suna Litil Boi, (Little Boy) a babban birnin kasar ta Jafan a lokacin, Hiroshima, wannan ya faru ne a ranar 6 ga Ogusta na 1945. Bayan kwana 3 da jefa na farko, wanda kasar Amurka tayi, sai ta sake harar birni na 2, wanda shine inda aka yi anfani da makamin Nukiliya na 2 a duniya, Ana cema Birnin Nagasaki. Ta jefa musu wani makamin Nukiliya mai dauke da makamashin Fulotoniyon, wanda Amurka ke mata lakabi da (Fat Man). Wannan ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu dari da ashirin 120,000, da wasu ‘yankai, wanda a sanadiyar tiririn hasken Nukiliyar mai dauke da guba dake shawagi a sararin samaniyar birnin da aka kai harin.
Tun bayan yakin duniya na biyu, ba a sake anfani da makamin na Nukiliya ba, saboda tsananin illar sa, da kuma barazana ga rayuwar wadanda basu dashi. Har ma ga wadanda suke da makamin abin na iya zama musu barazana domin kusan kullum suna cikin shirin ko ta kwana. Domin ita makamin na kunshe da abubuwa da yawa kamar haka, Manyan sinadaran kimiyya da ake amfani dasu wajen kera wannan makamin a Duniya sune makamashin Fulotiniyon, (Plutonium), da kuma Yuraniyom (Uranium). Ana dafa su ne har su kai wani mizani na zafi wanda ke chanza hakikanin su zuwa wasu Maddodin na daban, wanda zai kuma basu tasirin fashewa, ko hadewa da juna saboda alaka ko kusancin su da wasu makamashin haske ko maddodi daban. Saboda tsananin tasirin sa ga Tan guda a Nukiliya cikin makami, ko kwansonsa idan aka harba shi tasirin fashewar da kara da yawan sinadaran da zai fitar, dai-dai yake da tasirin Bom nazamani guda Biliyan daya (1 billion), kuma a lokaci daya, a wuri daya. Idan fashewar Nukiliya da mizamin sa yakai Tan Dubu, waton (1,000 Ton) ko sama da haka, to yana iya komawa da kuma tarwatsa Birni mafi girma a Duniyar Yau.
Sanadiyyar wani gamammiyar tasiri da wannan makamin ke dashi yasa ana masa lakabi da makamin kare Dangi, ko kuma (Weapon Of Destruction) a harshen turanci. Akalla kasashe 9 ne wadanda duniya ta tabbatar cewa sun mallaki wannan makamin; kasashen sun hada da kasar Amurka, Rasha, Faransa, Birtaniyya, Iran, Indiya, Pakistan, kasar Sin, da Kuma Koriya ta Arewa.
Akwai wasu kasashe kuma wadanda sun ki fitowa fili su nuna wa duniya cewa sun mallaki wannan makami, duk da cikakkiyar tabbaci da ake dashi kan sun mallaka, irin su kasar Isra’ila. Ko kuma wadanda zarginsu kawai ake cewa sun mallaka, amma babu tabbaci aan hakan, watakila saboda siyasar duniya ne. Kamar kasar Isra’ila misali, wacce ta ki fitowa fili ta nuna wa duniya cewa ta mallaki wannan makami kamar sauran kasashen duniya, kasar Amurka na da tabbacin cewa kasar Isra’ila ta mallaki wannan makami tun wajajen shekarar 1986, amma gwamnatin Amurka bata fito fili tayi magana wanda ya shafi hani ko goyon baya ba. Sai dai akwai rahotanni da wasu jaridun Ingila da na Amurka suka bayar, da ke nuna cewa kasar Isra’ila ta mallaki a kalla makamin Nukiliya kusan dari biyu (200).
Shin Nahiyar Afrika sun Mallaki wannan makamin kuwa?
Kuma me ya sa aka hana anfani da wannan makamin ta Nukiliya?
Me ya sa Majalisar dinkin Duniya suka yi yarjejeniya akan makamin ta Nukiliya?
Shin Nijeriya sun mallaki makamin ta kare dangi kuwa?
Za mu amsa wannan tambayoyi da mai karatu ya kamata ya san su a mako mai zuwa.
Comments
Post a Comment