Skip to main content

KIN JININ BAKI A AFRICA TA KUDU,ABUNDA KE FARUWA.

Wannan makala ce da aka rubuta don amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko kan hare-haren da ake kai wa baki a Afirka Ta Kudu. Sashen binciken kwaf na office Sashin basira Reality ne ya binciki lamarin.

A 'yan kwanakin da suka gabata, masu zanga-zanga sun tayar da zaune tsaye a birnin Johannesburg da ke Afirka Ta Kudu, inda masu zanga-zangar suka fasa shaguna da lalata motoci wadanda akasarinsu mallakar baki 'yan kasashen waje ne.

TAMBAYA: Mene ne Xenophobia?

AMSA: Xenophobia kalmar Turanci ce wadda ke nufin tsana ko kin jinin bakon abu, ko kuma a wannan yanayin mutane 'yan kasar waje. Kamus din Turanci na Merriam-Webster ya ruwaito cewa kalmar ta samo asali ne a karshen karni na 19.

Tambaya: Wai shin mai ya sa suke kin baki su 'yan Afirka ta Kudun kuma bakaken su ne kawai suke kin bakin ko kuma har ma fararen fata?

Amsa: Talauci da rashin aikin yi da ya yi wa 'yan kasar katutu shi ne kashin bayan wadannan hare-hare. Kasar ta samu cikas dangane da tattalin arzikinta, inda a hukamance aka bayyana cewa rashin aikin yi ya kai kusan kashi 27% a karshen shekarar bara. Kazalika, Afirka Ta Kudu na cikin kasashen da aka fi samun yawan kashe-kashe a duniya. Abubuwan da ke jawo hakan sun hada da talauci wanda wariyar launin fata da Turawan kasar ke nuna wa bakar fatar kasar, kamar yadda Sharon Ekambaram wani mai kula da shirye-shirye kan 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani ya bayyana.

Yawan hare-haren ya sa an fito da tsare-tsare domin kawo karshen wariya ko kuma kin jinin baki

Tambaya: Shin yaushe 'yan kasar Afirka Ta Kudu suka fara wannan al'adar ta kai wa baki hari? Sannan gwamnatin kasar ta taba daukar wani matakai ne?

Amsa: Wani rahoto ya bayyana cewa hare-haren sun yi kamari ne a 2008 da kuma 2015. A 2008, an yi ta samun hare-hare nan da can kan 'yan gudun hijira da kuma 'yan ci-rani - an bayyana cewa an kashe fiye da mutane 60 an kuma raba dubbai da muhallansu. A 2015, an kai hari ga baki da dama wadanda ba 'yan asalin Afirka Ta Kudu ba ne, akasari a garuruwan Johannesburg da Durban wanda hakan ya jawo kai jami'an sojojin kasar domin kwantar da tarzoma.

Tambaya:A wane yanki hare-haren suka fi kamari?

Amsa: Lardin Gauteng, wanda ya hada da birni mafi girma a Afirka Ta Kudu wato Johannesburg da kuma babban birnin kasar Pretoria, suke da mafi yawan hare-haren da aka kai. Sai kuma yammacin birnin Cape kamar yadda cibiyar da ke kula da 'yan ci rani ta Afirka ta shaida. KwaZulu-Natal ne yanki na uku.

Hare-haren sun fi yawa ne a manyan biranen kasar, amma akwai wasu rahotanni da ke cewa an kai hare-haren a kananan garuruwa da kuma karkara. Akasarin rikice-rikicen na farawa ne daga musayar yawu tsakanin 'yan kasar da baki har lamarin ya girma ya fadada. An fasa shaguna da dama na baki kuma an sace kayayyakinsu.

Tambaya: 1. Shin wanne irinn mataki hukumar kasar ta dauka domin magance irin wannan matsalar? Wadanda abin ya shafa ya za a yi da su? Wane irin taimako za a ba su? 2. Wane mataki gwamnatin Afirka Ta Kudu ke dauka kan wannan cin mutuncin da ake yi wa baki?

Amsa: Wani bangare na jami'an Afirka Ta Kudu sun bayyana cewa hare-haren ba na kin jinin baki ba ne, masu aikata laifuka ne kawai suke kai hari. Shi ma Shugaban Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da hare-haren, inda ya bayyana cewa babu wata doka a kasar da ta ba da dama a kai hari ga baki mazauna kasar. Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta aika takardar sammaci ga jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu. Kazalika, Najeriya ta kaurace wa wani taron tattalin arziki na duniya wato World Economic Forum da ake yi a kasar, wanda a da ta yi niyyar halarta.

Ministar harkokin wajen Afirka Ta Kudu Lindiwe Sisulu, ta bukaci jami'an 'yan sanda ta dauki mataki kan masu kai hare-hare. Shi ma ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, a wani taron manema labarai, ya bayyana cewa "Wajibi ne a biya diyya ga wadanda abin ya shafa kuma za mu yi bakin kokarinmu kan hakan." A watan Maris, gwamnatin kasar ta fitar da wani sabon tsari domin kara wayar da kan jama'a kan taimakon wadanda lamarin nuna wariya ko kuma kin jini ya shafa.

Hukumomin kare hakkin bil adama sun karbi wannan tsarin hannu biyu-biyu, sai dai kungiyoyin sun bukaci gwamnatin kasar da ta ayyana hare-haren da 'yan kasar suke kai wa ga baki a matsayin na kin jini. A wata sanarwa da aka wallafa a watan Oktoban 2018, babbar jam'iyyar hamayya a Afirka Ta Kudu wato ''Democractic Alliance,'' ta dora laifi ga jam'iyya mai mulki ta ANC kan hare-haren da ake kai wa wadanda ta ce na kin jinin baki ne.

Xenophobia: 'Yan Najeriya za su kauracewa kayan Afirka ta Kudu 'Yan kasuwa da 'yan sandan Afirka ta Kudu na gumurzu Aisha Buhari ta ja kunnen masu rike da mukamai

Tambaya: 1. Su wane ne ke kai wa baki hari a Afirka ta Kudu da gwamnati ba za ta iya hukunta su ba? Ganin cewa a bainar jama'a suke tafka barnar. 2. Mene ne ainihin musabbabin kai wadannan hare-hare, kuma shin iyaka kan 'yan Najeriya ne ko har da sauran wasu kasashe. A wanne gari ne aka fi yi?

Amsa: Gwamnatin Afirka Ta Kudu ba ta da cikakkiyar kididdiga kan hare-haren da ake kai wa baki, kuma da alama gwamnatin ba ta da wannan kididdiga ma kwatakwata. Lardin Gauteng, wanda ya hada da birni mafi girma a Afirka Ta Kudu wato Johannesburg da kuma babban birnin kasar Pretoria, su ke da mafi yawan hare-haren da aka kai. Sai dai, cibiyar da ke kula da 'yan ci rani ta Afirka wato African Centre for Migration & Society ta bi kadin wadannan hare-haren a Afirka Ta Kudu tun daga shekarar 1994. Bayanan da cibiyar ta tattara kan hare-haren sun hada da bayanai daga kafofin yada labarai da kuma bayanai daga 'yan gwagwarmaya da wadanda lamarin ya shafa da sauran masu sa ido.

Tambaya: Assalam alaikhum, shin wannan harin da ake kai wa baki iya 'yan Najeriya ya shafa ko akwai sauran 'yan kasashen waje? Sannan mene ne dalilin hakan?

Amsa: Hare-haren da ake kaiwa sun shafi dukkanin bakin da ke zaune a kasar. Yawan 'yan Najeriya a kasar ya kai 30,314, kamar yadda rahoton kididdiga daga wani bincike mai suna 2016 Community Survey wanda aka fitar a 2016 ya nuna. Tsagerun da ke kai wadannan hare-hare suna kallon duk wani bakar fata bako a matsayin dan Najeriya.

Rikicin baya-bayan nan ma ya fara ne ta dalilin wani dan kasar Tanzania da wasu matasa suka hana shi sayar da kwaya, inda shi kuma ya ki ji, abin da ya sa su kuma suka rufe shi da duka har ma suka yi masa rauni. Daga baya shi kuma ya dauko bindiga ya harbi daya daga cikin wadanda suka yi masa raunin. Daga nan ne kuma 'yan uwansa masu tukin motar tasi suka far wa 'yan Najeriya da kuma sauran 'yan kasashen waje.

Kashi 70 cikin 100 na baki da ke Afirka Ta Kudu sun taho daga Zimbabwe da Mozambique da kuma Lesotho ne. Sauran kashi 30 kuma cikin 100 sun taho ne daga Malawi da Ingila da Namibia da eSwatini (Swaziland a da) sai kuma Indiya da kuma sauran kasashe. Mai magana da yawun hukumar kididdiga ta Afirka Ta Kudu ya shaida wa Sashin basira cewa akwai akalla 'yan gudun hijira ko kuma baki miliyan 3.6 a kasar cikin mutum miliyan 50.

Kasar ta samu cikas dangane da tattalin arzikinta inda a hukamance aka bayyana cewa rashin aikin yi ya kai kusan kashi 27 cikin 100 a karshen bara. Kazalika kasar na cikin kasashen da aka fi samun yawan kashe-kashe a duniya.

         DAGA
    SANI ABUBAKAR DIKUWA
              08168604297

Comments

Popular posts from this blog

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da y...

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All...

ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM KASHI NA BIYU

 Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2) DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin. A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin ƙoƙon kai, da kuma wadda ke ƙasan ƙeya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take ƙasanta, wadda ta haɗe da laaka dake gadon bayan mutum. Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin ƙoƙon kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta ɓari biyu ce: ɓarin hagu da ɓarin dama. Wasu masanan sun ce aikin da ƙwaƙwalwar dama ta ke yi...