Skip to main content

KADAN DAGA TARIHIN BABBAR KASUWAR GOMBE

Kasuwa dai gurine da ake hada-hadar kayayyaki na saye da sayar wa, kuma gurine dake tara mutane maban-bamta, kuma kasuwa tana bunkasa ne daga yawaitar mutanen dake shige da fice daga cikinta. Wadanda suka hada da mutanen kar-kara masu kawo kaya, da masu Sayan kayan.
      Yau zamu tsakuro muku tarihin babbar kasuwar Gombe dake arewa maso gabashin Nigeria. Babbar kasuwar dai ta wanzu wajejen shekaru 36 baya. To tun sheka(1983) kuma ta tasone daga tsohuwar kasuwar dake tsakiyar fadar jihar,wato kudu maso yammacin gidan Sarkin Gombe. Inda kasuwar take a yanzu ya kasance gona ce ta Sarki a da can, sannan ta farane daga yamma da inda take yanzu, wato wa danda suka fara dawowa sune MAHAUTA sannan daga baya suka koma arewacin kasuwar, sai kuma yan Gwari suka zauna a yammacin kasuwar, a kudancin kasuwar ya dauki yan kasuwa masu caton-caton, da suka hada da provision. Abaya kasuwar ta kasnce ne shagunan kwano na langa-langa. Ayanzu dai kasuwar ta girma sosai domin ta iso duk wani guri da aka zaba a matsayin kasuwar na farko. Sannan daga gabar tayi iyaka ne da tashar jirgin kasa ta jahar, a yamma kuma tayi iyaka da titin Bello sabon kudi,,a arewa kuma tayi iyaka ne da babban filin Idi,na fadar jihar, a kudu kuma kasuwar tayi iyaka ne da Babban gidan mai na NNPC wato mega station. Kasuwar ta Gombe tayi fama da masifu na gobara da dama wadanda suka haddasa asarar dukiyoyi da dama, kusan ko wanne bangare na kasuwar ya gamu da irin nasa bala'in, na kwana-kwanan ma shine Wanda wuta ta kama wasu shaguna a kasuwar waya da ake arewacin kasuwar.
A kwai  Tsofaffin yan-kasuwar da suka hada:   Alh.HUSSAINI MAI YADI.
            Alh.JAURO BAPPHI.
            Alh.SAIDU MARAFAN TUMU.
            Alh.IBRAHIM MAI ZARE.
            Alh.ADAMU MALAM.
            Alh.SALEH MAINA.
da sauransu da dama .Sannan a yanzu kasuwar ta fafe yayanta da dama,domin tana dauke da manya-manyan diloli, da manyan yan-kasuwar masu karfin jarin da ake al-fahari dasu a arewa maso gabashin kasar.
Kamar su :Alh.SA'ADU MAI SILIFAS.
                   Alh.IBRAHIM MAGINI.
                   Alh.DOGON RUWA.
                   Alh.SANI HUSSAIN.
                   Alh.UMARU YARO
                   Alh.BUBA YARO.
                   Alh.UBA ABDULLAHI.
                   Alh.ABBAKAR MIGINI.
                   Alh.SADIQU SHEHU.
                  Alh.SULAIMAN MAI KUSA Wanda shine Chairman na  kasuwar a yanzu.
Sannan kusan babu abunda kasuwar bata fitarwa, kumai ya shiga kasuwar zai karbu,sabo da yadda kasuwar ke tafiya.

Labari daga: Mal.Muhammadu, Wanda akafi sani da HAMMA BOSSE. Daya daga cikin wadanda suka bude kasuwar.

Tsara Rubutu: Alh.Adamu waziri shamaki.

Rubutawa:: Sani Abubakar Dikuwa.
 
                      08168604297
          
                

Comments

Popular posts from this blog

Falalar Azumi.

 DAGA: Sani Abubakar Dikuwa. Bismillahirrahmanirrahim, Ina mana maraba da zuwan wata mai alfarma watan Ramadan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu. Bayan Haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki: * Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277] * Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280] * Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7] * Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904] * Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da y...

FALALAR AZUMI.

FALALAR AZUMIN WATAN RAMADAN Falalar watan azumin Ramadan da irin rahman da ke cikinsa DAGA: Sani Abubakar Dikuwa Azumin Ramadan na da falala da yawa. A cikin wannan wata na Ramada ne aka fara saukar wa da fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) da littafi mai tsarki. Saboda tsarkin wannan wata ne ake rufe duk wani shaidani da kofofin gidan wuta sannan a bude kokofin gidan Al-jannah. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- 1. Azumin Ramadan na kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace: Manzon Allah {S.A.W} yace: "Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).” 2. Ya zo a hadisin Abi Umamata (R.A.) yace: "Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578). 3. Azumi kuma shine Musababin tsoron All...

ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM KASHI NA BIYU

 Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2) DAGA: SANI ABUBAKAR DIKUWA ‘Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana, Amin. A rubutun da mukayi a baya, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku. Akwai wadda ta cinye ilahirin ƙoƙon kai, da kuma wadda ke ƙasan ƙeya daidai inda wuya ya hadu da kai ta baya, da kuma wadda take ƙasanta, wadda ta haɗe da laaka dake gadon bayan mutum. Mafi girma daga cikinsu ita ce ta farkon, wadda ta cinye dukkanin ƙoƙon kai. A turance ana kiranta da “cerebrum”. Ita kanta ɓari biyu ce: ɓarin hagu da ɓarin dama. Wasu masanan sun ce aikin da ƙwaƙwalwar dama ta ke yi...