Annabi muhammad (SAWA) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanakin goman farkon watan Dhu al-Hijjah Malamai na ci gaba da fadakar da al'ummar Musulmi dangane da falalar kwanaki goman farko na watan Dhul Hijjah, Musulmi dai na daukar kwanaki goman farko na wannan watan a matsayin mafi daraja a wajen Allah. Hadisi ya zo cewa Annabi Muhammad (SAW) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanaki goman farkon watan Dhu al-Hijjah. Akwai kuma ibadu da ɗabi'u da Musulmi ke siffantuwa da su a cikin wadannan ranakun da suka haɗa da yin azumi da hawan Arfa da kuma layya domin neman kusanci ga Allah Ubangiji. Sheikh Sani yahaya Daban-fulani, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya ya yi wa mana bayani kan muhimmancin watan na Dhu al-Hijjah da kuma abubuwan da ya kamata Musulmi suyi KADA A ASKE GASHI, DA YANKE FARCE Abu na farko shi ne idan mumutum yana da niyyar zai yi layya, to daga daya ga watan Dhu al-Hijjah kada ya yank...