Assalamu alaikum. Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci. Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne. Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba. Masu wannan fahimtar Malamai sun ce ba wai suna nufin a koma wa Sunnar Manzon Allah ba ne, suna so ne a koma wa zamanin Annabi (SAW), ka ge ke nan sai mu ajiye su motoci da sauran kayan kere-kere na fasaha sda ake amfani da su yanzu har da su lantarki da su jirgin sama duk a ajiye, a koma amfani da su rakuma da dawaki da jakuna. Idan kayan yaki ne ma a ajiye su nukiliya, da manyan tankokin yaki da su jiragen yaki sai dai a yi amfani da su kwari da baka da takubba, idan an tari abokan gaba da wadannan an yi bidi’a kamar yadda fahimtar wadancan mutanen take. Ka ga idan aka yi haka ai hankali ya warware. Kur’anin da Allah ya saukar mana zamaninsa ba ya shudewa, ya dace da kowane irin zamani da ya zo, ko zai z...