Kasuwa dai gurine da ake hada-hadar kayayyaki na saye da sayar wa , kuma gurine dake tara mutane maban-bamta , kuma kasuwa tana bunkasa ne daga yawaitar mutanen dake shige da fice daga cikinta . Wadanda suka hada da mutanen kar-kara masu kawo kaya , da masu Sayan kayan . Yau zamu tsakuro muku tarihin babbar kasuwar Gombe dake arewa maso gabashin Nigeria. Babbar kasuwar dai ta wanzu wajejen shekaru 36 baya . To tun sheka (1983) kuma ta tasone daga tsohuwar kasuwar dake tsakiyar fadar jihar , wato kudu maso yammacin gidan Sarkin Gombe . Inda kasuwar take a yanzu ya kasance gona ce ta Sarki a da can, sannan ta farane daga yamma da inda take yanzu , wato wa danda suka fara dawowa sune MAHAUTA sannan daga baya suka koma arewacin kasuwar , sai kuma yan Gwari suka zauna a yammacin kasuwar , a kudancin kasuwar ya dauki yan kasuwa masu caton-caton , da suka had...